Gwamnan Imo ya shawarci 'yan adawa su shigo APC idan ba su son cigaba da zama da 'yunwa'

Gwamnan Imo ya shawarci 'yan adawa su shigo APC idan ba su son cigaba da zama da 'yunwa'

- Gwamnan Imo Hope Uzodinma ya yi wa 'yan siyasar jam'iyyun hamayya tayin shigowa jam'iyyar APC mai mulki

- Uzodinma ya ce idan har suna son fitar da mutanen jihohinsu daga kangin yunwa ya kamata su shigo jam'iyyar mai mulki

- Gwamnan na Imo ya ce babu shakka kasancewa tare da jam'iyya mai mulki yana saukaka yadda dan siyasa zai warware matalolin al'ummarsa

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya yi kira ga 'yan siyasa da ke jam'iyyar adawa su shigo jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ko kuma su cigaba da fama da 'yunwa'.

Ya bayyana hakan na a babban birnin tarraya Abuja a yayin da ya ke martani kan komowar gwamnan Ebonyi Dave Umahi da ya fice daga PDP ya dawo APC, Premium Times ta ruwaito.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari, Mista Uzodinma ya ce Mista Umahi "ya fahimci cewa shigowa jam'iyyar APC zai fitar da jiharsa daga cikin kangin yunwa."

Ku shigo APC ko kuma yunwa ta kashe su, in ji Uzodinma
Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Hope Uzodinma. Hoto daga @Buharisallau1
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

"Idan kai kayi imani da Najeriya daya kuma kana da ra'ayin kishin Najeriya tabbas zaka shigo jam'iyya mai mulki. Babu wata jayayya kan cewa idan baka tare da jam'iyya mai mulki, ka zabi cigaba da zama a jam'iyyar adawa, tabbas zaka cigaba da azumi ne har sai Allah ya amsa addu'oin ka.

"Amma mu kam muna cikin jam'iyya mai mulki, akwai banbancin kan yadda zamu iya warware wasu matsalolin mu idan an kwatanta da wadanda ba su kusa da inda mulki ya ke."

Har wa yau, Mista Uzodinma ya cigaba da cewa APC ita ce jam'iyyar kasa kuma yana fatan wasu za su sake shigowa jam'iyyar.

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

Ya ce ba zaka kwakwanta alherin al'ummarka za su samu ba idan kana tare da jam'iyyar da ke mulki a maimakon ta hammaya kana ya ce abinda ya ke fata kullum shine ganin hadin kan Najeriya ba tare da la'akari da bangaranci ba.

"Jam'iyyar APC itace wacce ta fi dukkan sauran wurin tsare-tsare masu kyau kuma ita ke da mulki a hannun ta," in ji shi.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel