Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

- Hukumar Hisbah na ci gaba da kokarin tabbatar da shari'ar musulunci a arewa duk da rashin goyon bayan wasu yan Najeriya

- Hukumar ta Hisbah ta gudanar da bincike ɗaki ɗaki a wurin shakatawa na Hills and Valley da ke birnin Kano ranar Juma'a don kama masu badala

- Ko a farkon watan nan, hukumar ta fasa kwaleben giya na sama da miliyan 300 a jihohin Katsina Kano da Kaduna

Jami'an hukumar Hisbah a Jihar Kano ranar Juma'a sun gudanar da wani binciken kwakwaf a Hills and Valley, wani wajen yawon bude ido da shakatawa a Dawakin Kudu, da ke birnin Kano.

SaharaReporters ta ruwaito cewa an tilasta ma'aikatan wajen su zagaya da jami'an Hisbah duk gine ginen da ke wajen.

Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu baɗala a Kano
Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu baɗala a Kano. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu badala a Kano
Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu badala a Kano. Hoto daga @SaharaReporters
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

Lokacin binciken, jami'an Hisbah sun duba ko wane daki da sauran wurare don gano masu aikata 'badala'.

Duk da wasu yan Najeriya ba sa goyon baya, hukumar Hisbah na ci gaba da kokarin kafa aƙidun musulunci a arewa.

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu baɗala a Kano
Hisbah ta yi bincike gida-gida don kama masu baɗala a Kano. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

Hukumar ta kirkiri kafa dokokin musulunci a wasu jihohi, sun hana sun hana askin banza, ɗame wando, hana kaɗe kaɗe lokacin shagali da ƙwace Adaidaita da aka yi wa ado da hotunan da suka saɓa da tarbiyar musulunci.

Hukumar ta kuma hana daukar mata biyu a baburin haya guda daya.

A farkon watan nan, hukumar ta fasa kwalaben giya da suka haura naira miliyan 300 a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.

A wani labarin, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel