Yaudararmu kayi muka zabeka - Dattawan Jihar Neja ga Buhari

Yaudararmu kayi muka zabeka - Dattawan Jihar Neja ga Buhari

- Kamar yadda Buhari yayi umurni, Ministocinsa sun fara ganawa da al'ummominsu a madadinsa

- Ganawar Ministan da ya fito daga Neja ba tayi dadi ba bisa kalaman da al'ummar sukayi kan mulkin Buhari

- Ambasada Zubairu Dada ya tara manyan masu ruwa da tsakin jihar domin tattaunawa da su da yawun Buhari

Masu ruwa da tsaki a jihar Neja sun zargi shugaba Muhammadu Buhari da yaudaransu duk da dubunnan kuri'un da suka bashi a zaben 2015 da 2019, Dailypost ta ruwaito.

Sun bayyana cewa babu abinda Buhari ya tsinana musu tun lokacin da ya hau mulki.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Minna a taron da karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, ya shirya.

Wadannan masu ruwa da tsakin sun hada da yan majalisu, sarakunan gargajiya, kungiyoyin matasa, kungiyoyin mata, da malaman addini.

Duka sun bayyana ra'ayoyinsu kan irin kalubalen da jihar ke fuskanta.

Sun bayyana yadda suke fama da hare-haren yan bindiga, rashin hanyoyi masu kyau, da rashin wutan lantarki.

KU KARANTA: An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone

Yaudararmu kayi muka zabeka - Dattawan Jihar Neja ga Buhari
Yaudararmu kayi muka zabeka - Dattawan Jihar Neja ga Buhari Hoto: Taswirar Neja
Asali: UGC

KARANTA: Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

Shugaban matasan jihar, Bello Sharif, ya ce shugaba Buhari ya yaudari jihar duk da irin goyon bayan da ya samu lokacin zabensa na farko da na biyu, amma daga baya yake hanasu romon demokradiyya.

"Muna fushi da shugaba Buhari, muna son shi amma shi baya son mu. Ya yaudare mu. HYPPADEC da tashar Baro ba su aiki, titunan jihar kilomoya 2000 sun lalace, dss, " yace

"Shi yasa muke kira ga ministoci da yan majalisu su kawo mana dauki, kuma idan basu yi haka ba, idan suka kiramu, matasa Neja ba zasu sauraresu ba."

Babban Limamin Minna, Malam Ibrahim Fari, ya ce rashin tsaro da rashin wutan lantarki na daga cikin manyan matsalolin da jihar ke bukata.

"Muna son AEDC ya kara mana wutan lantarki a jihar. Ba zamu amince da wuta kasa da sa'a 20 a rana ba, idan ba zasu iya bamu ba, su fita daga jiharmu, " ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel