Yan bindiga sun hallaka Maigari, Soja da wasu mutane 18 a jihar Katsina

Yan bindiga sun hallaka Maigari, Soja da wasu mutane 18 a jihar Katsina

- Har yanzu, yan bindiga da cigaba da cin karnukansu ba babbaka a jihar Katsina

- Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu wannan karon akwai jami'in Soja

- An samu nasarar fanso wadanda suka sace bayan kwanaki biyu

Yan ta'adda a jihar Katsina sun kone kauyen Diskuru dake karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina kurmus, yayinda suka hallaka akalla mutane 20.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai Maigari, jami'in Soja, mata da yara.

Jaridar HumAngle ta ruwaito cewa yan ta'addan sun dira kauyen ne da safiyar Alhamis, 29 ga Oktoba inda suka lalata gidaje akalla 60, suka kashe mutane, kuma sukayi awon gaba da wasu.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai Maigari, Alhaji Sama’ila Hussaini; yaro dan shekara 12, Sanusi Sani, da kananan yara mata 2, Hanafiya Dauda da Asiya Maikara.

Sauran sune, Bishir Auwal (36), Anas Dan-yaya (29) Sule Dan-Yaya (27), Aminu Bala (40), Nura Abashe (36), Mai-‘Kaura Amadu (68), and Sa’idu Kurma Surajo (40).

Matan da suka rasa rayukansu sun hada da Zaytu Dan-yaya (36), Nana Sagiru (20), Abu Dauda (25) da Sahu Mai kara (20).

Yan bindiga sun hallaka Maigari, Soja da wasu mutane 18 a jihar Katsina
Yan bindiga sun hallaka Maigari, Soja da wasu mutane 18 a jihar Katsina Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Isah Gambo ya tabbatar da aukuwan lamarin amma yace mutane 12 aka kashe.

A cewar mazaunan gari, an samu nasaran ceto dukkan wadanda aka sace bayan tattaunawa da yan bindigan.

A bangare guda, wasu yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari garin Gidan Gog0a dake karamar Maradun na jihar Zamfara, inda mutane akalla hudu suka rasa rayukansu.

Mazauna sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira garin kan babura suna harbin mutane kafin sukayi awon gaba da shanu da awaki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai inda yace harin ya faru ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel