Yau wace rana: Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya yabawa shugaba Buhari

Yau wace rana: Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya yabawa shugaba Buhari

- Abin mamaki a cewar wasu, shugaban jam'iyyar adawa ya yabawa shugaba Buhari

- Secondus ya jinjinawa Buhari saboda ya ajiye siyasa gefe wajen zaben Okonjo-Iweala

- Tsohuwar ministar kudi na Najeriya na gab da zama mace ta faro da zata zama shugabar kungiyar kasuwancin duniya

Jam'iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) ta jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da ya nunawa Dr Ngozi Okonjo Iweala a takaran da take yi na shugabancin kungiyar kasuwancin duniya WTO.

Shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, yayi wannan jinjinawan a jawabin da mai magana da yawunsa, Mr Ike Abonyi, ya saki ranar Laraba, Vanguard ta ruwaito.

Secondus ya ce Najeriya za ta kafa tarihi idan Okonjo-Iweala ta zama mace ta farko a duniya da zata zama shugabar kungiyar WTO.

Ya yabawa shugaban Buhari kan ajiye siyasa gefe da yayi wajen goyawa Okonjo-Iweala baya da kuma Dr Akinwumi Adesina, shugaban bankin cigaban Afrika (AfDB) bayan da yayi har suka samu nasara.

Ya ce nasarar Okonjo Iweala na zuwa ne bayan tazarcen Adesina matsayin shugaban bankin AfDB, kuma hakan ya farantawa PDP rai saboda dukkan wadannan mutane biyu tsaffin Ministoci ne a gwamnatin PDP.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17

Yau wace rana: Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya yabawa shugaba Buhari
Yau wace rana: Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya yabawa shugaba Buhari Credit: @Vanguard
Asali: Twitter

Mun kawo muku cewa Tsohon ministar kudin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo Iweala na gab da zama sabuwar Dirakta Janar na kungiyar kasuwancin duniya.

A cewar majiyoyi daga gamayyar kasashen Turai, za ta zama shugabar kungiyar ne bayan nasara kan Yoo Myung-hee, yar kasar Koriya ta kudu, idan akayi zaben ranar 9 ga Nuwamba.

Kasashe 27 da ke karkashin kungiyar Turai ta EU su na goyon bayan tsohuwar ministar tattalin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a zaben WTO.

DUBA WANNAN: Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel