Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa

Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa

- Kasashen Musulmai sun yi Allah-wadai da gwamnatin kasar Faransa

- Shugaban kasan Faransa ya ce kowa zai iya abinda ya ga dama a kasar ko da isgili ga Manzon Allah ne

- Turkiyya ta yi hannun riga da Faransa

Gwamnatin Saudiyya ta ce "ba zata lamunci kokarin hada addinin Musulunci da ta'addanci ba kuma ta yi Alla-wadai da zanen manzon Allah domin bakantawa wasu rai."

Saudiyya ta bayyana hakan ne yayinda kasashe Musulmai ke caccakan kasa Faransa bisa goyon bayan zanen isgili ga manzon Allah SAW da shugaban kasan ya amince a rika yi.

Saudiyya ta yi kira ga Faransa da shugabanta su koyi girmama ra'ayoyin mutane da kuma zaman lafiya maimakon amincewa da abubuwan da ka iya tayar da tarzoma da haifar da kiyayya tsakanin al'umma.

Wani ma'aikacin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ya bayyana hakan a gidan talabijin kasar ranar Talata, Aljazeera ta ruwaito.

Ya kara da cewa Saudiyya na Allah-wadai da dukkan wani aikin ta'addanci da wani zai yi saboda hakan ba koyarwan addinin Musulunci bane.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa
Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa
Asali: Facebook

KU DUBA: Bata gari sun kai hari sansanin NYSC na Abuja, suna wawan katifu

Hakazalika, shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira kasashen duniya su kauracewa sayan kayayyakin da ake yi a Faransa yayinda majalisar dokokin kasar Pakistan ta bukaci jakadanta dake Faransa ya dawo gida.

Bugu da kari, kungiyoyin kasuwanci daban-daban na kasashen Larabawa sun alanta yanke alaka ta kasuwanci da Faransa.

An yi zanga-zanga a kasashe irinsu Iraqi, Turkiyya, Falasdin, inda aka kona hotunan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.

A Saudiyya, an yi kira ga kauracewa shagon Faransa, Carrefour, a dandalin ada zumunta.

Amma ita gwamnatin bata yi kira ga hakan ba.

Mun kawo muku rahoton cewa wani dalibin makaranta ya fille kan malaminsa bayan ya yi zanen isgilanci ga Annabi Muhammad a harabar makarantar ranar Juma'a.

Matashin ya nuna alfaharinsa na rashin iya jure ganin ana batanci ga manzon Allah yayi shiru.

Har yanzu ba'a bayyana hotonsa ba amma jami'an yan sanda sun bude masa wuta kuma suka kasheshi, a cewar Reuters.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel