Sabbin mutane 119 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 62,111

Sabbin mutane 119 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 62,111

- Hukumar NCDC ta bayyana dalilin da ya sa ta daina sakin adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar Korona a shafukanta na Facebook da Tuwita

- An yi haka ne domin karrama zanga-zangar EndSARS da matasa ke yi a fadin Najeriya

- Yanzu hukumar ta dawo wallafawa kamar yadda ta saba

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 119 ranar Juma'a a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 61,882 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Litinin, 27 ga watan Oktoba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane sama da 62,000 da suka kamu, an sallami 57,571 yayinda 1132 suka rigamu gidan gaskiya.

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu– Lagos-77, FCT-26, Plateau-9, Edo-4, Oyo-2, Nasarawa-1.

KU KARANTA: Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu

Sabbin mutane 119 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 62,111
Sabbin mutane 119 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 62,111 Credit: @NCDC
Asali: UGC

KU DUBA : Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

Kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, ta shiga jerin masu kira ga matasa masu zanga-zangar #ENDSARS su sassauta kuma su amince da sulhu saboda har yanzu akwai cutar Korona a gari.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hira da manema labarai a Abuja, The Sun ta nakalto

Mustafa ya siffanta masu zanga-zangan a matsayin manyan masu iya yada cutar kuma za'a fara ganin sakamakon hakan nan da makonni biyu masu zuwa.

"Maganar gaskiya shine, nan da mako biyu masu zuwa, idan ka tattara dukkan masu taro a Lekki Toll Plaza, za ka samu masu cutar da dama, " Mustafa yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel