Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi

Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi

- Jama'a fusatattun a jihar Kogi sun balle ma'adanar kayayyakin tallafi

- Lamarin ya faru a jihar Kogi a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020

- Matasan sun gano inda aka adana tallafin ba tare da an raba musu ba

Mazauna jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya sun fasa ma'adanar kayan tallafin COVID-19 da aka bai wa jihar.

Kamar kowacce jihar, sun kwashi iyakar kayan da za su iya kwasa sannan suka yi awon gaba da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Balle wuraren adana tallafin korona a jihohi ya fara daga yankin kudancin kasar nan bayan zanga-zangar EndSARS.

Lamarin ya cigaba da shigowa jihohin arewa inda fusatattun matasa ke nemo ma'adanar kayan rage radadin.

Sakamakon yawaita balle ma'adanar kayayyakin tallafin, gwamnatocin jihohi daban-daban sun saka dokar ta-baci.

Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi
Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda

Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi
Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi
Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi
Hotunan matasa suna wawushe tallafin korona a Kogi. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

A wani labari na daban, bata-gari sun cigaba da yadda suka ga dama da dukiyoyin gwamnati da na al'umma sakamakon barkewar rikicin zanga-zangar EndSARS, Daily Trust ta wallafa.

A jihar Benin, Anambra, Edo, Kaduna, Filato, Cross River da Ekiti, matasa sun yi ta shiga ma'adanai, inda aka ajiye kayan tallafin COVID-19, wadanda ya kamata a raba wa talakawa, suna awon gaba da su.

Manema labarai sun tattaro bayanai a kan yadda mutane 5 suka rasa rayukansu a jihar Edo, 5 a jihar Taraba da kuma wani mutum a Anambra, duk sakamakon kwasar kayan abincin.

Wasu matasa sun kwashi buhunan kayan abinci bayan balle kofofin ma'adanar kayan tallafin COVID-19 na gwamnatin jihar Filato dake Jos a ranar Asabar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel