Yanzu-yanzu: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni 58 (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni 58 (Hotuna)

- Karo na biyar cikin kwanaki biyu, matasa sun balla gidan yari a jihar Ondo

- Hukumar gidajen ta tabbatar da adadin fursunonin da aka saki

- Babu wanda ya rasa ransa kuma ba'a kama kowa ba har yanzu

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa wasu matasa sun kai hari gidan gyaran halin jihar Ondo kuma sun saki fursunonin dake ciki.

Bidiyon da wani Fasanmi Paul ya daura shafins ana Facebook ya nuna yadda fursunonin ke kokarin fitowa.

A cewar rahoton Channels TV, akalla fursunoni 58 sun gudu daga gidan gyara halin kuma sun bankawa gidan yarin wuta dake karamar hukumar Ikitipupa na jihar.

A cewar rahoton, kakakin hukumar yan sandan Ondo, ASP Tee Leo-Ikoro ya tabbatar da hakan a hirar wayar tarho.

A cewar masu idanun shaida, wasu jami'an tsaro sun samu rauni amma babu tabbaci ko an rasa wani tukun.

DUBA NAN: PDP ta shigar da karar INEC da Gbajabiamila bayan jigo a jam'iyyar ya koma APC

Yanzu-yanzu: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni 58 (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni 58 (Hotuna) Hoto: APC Secretariat
Asali: Facebook

Ga jerin gidajen yarin da aka balla kwanan nan:

1. Gidan yarin Warri da ke jihar Delta

Mun samu labarin cewa fursunoni sun saka wuta a wani bangare na gidan yarin Warri da ke kan titin Okere a jihar Delta.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta kasa (NCS), DSP Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kara da cewa mahukuntan gidan yarin ba su da masaniyar ko wani Fursuna ya tsere.

The Nation ta ruwaito cewa wasu Fursunoni da ba a san adadinsu ba sun tsere daga gidan yarin na Okere duk da harbe-harben da jami'an tsaro ke yi.

2. Gidan yarin Ikoyi da ke jihar Lagas

A yau Alhamis ne jami'an yan sanda da Sojoji suka dira gidan gyaran halin a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas domin dakile yunkurin fitar da fursunoni da wasu bata gari ke yi yanzu haka.

An gano wasu bangarori na kurkukun na ta ci da wuta yayinda mutanen yankin ke neman mafaka don tsiratar da rayuwarsu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sai dai bata garin basu cimma manufarsu ba domin jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin.

3. Gidajen yari na Benin da Oko a jihar Edo

A ranar Litinin ne hukumar gyaran gidan hali ta Najeriya ta tabbatar da harin gidajen yari a hanyar Sapele da ke Benin da Oko duk a jihar Edo, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Fursunoni 1,993 ne suka gudu bayan harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel