Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi

Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi

- Fatima Ganduje -Ajimobi, diyar gwamnan jihar Kano, ta yi wallafa inda ta nuna damuwarta

- Ta bayyana cewa, ta rasa me za ta ce amma tana matukar jin kunyar abinda tayi

- Ta yi nadamar taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma rashin kishin kasa

Diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Fatima Ganduje Ajimobi, wacce ke auren dan marigayin tsohon sanata kuma gwamnan jihar Oyo, ta yi magana a kan shugabanni.

Fatima Ganduje Ajimobi ta ce ta rasa me za ta ce a wallafar da tayi amma tana matukar nadama.

Ta bayyana damuwarta tare da dana-saninta na goyon bayan shugabanni "marasa hankali kuma marasa kishin kasa."

Kamar yadda ta wallafa, "Na rasa me zan ce kuma ina matukar jin kunya da na taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma kishin kasa."

Fatima ta yi wannan wallafar ne bayan sa'o'i kadan da yin harbe-harbe ga masu zanga-zangar bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan sanda ke yi a Lekki tollgate da ke jihar legas.

Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi
Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Matasa sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan.

Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani.

A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame.

"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai," sakon yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel