Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 22

Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 22

- Kaman an samu sauki, yan bindiga sun cigaba da halaka mutane a Zamfara

- Watanni bayan gwamnatin jihar ta shiga sulhu da yan bindigan jihar

- Irin haka bai daina faruwa a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto ba

Yan bindiga sun hallaka akalla mutane 22 a garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020, The Punch ta ruwaito.

Wani dan garin, Malam Ahmed Mohammed ya bayyanawa wakilin Punch cewa yan bindiga sama da 100 sun kai farmako kauyen misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbe-harbe.

Yace: "Mutane ashirin da biyu, wanda ya hada da mata da yara aka kashe lokaci guda, yayinda wasu suka gudu cikin daji."

Mohammed ya kara da cewa mutane da dama sun jiggata sakamakon harbi kuma an garzaya da su asibiti domin jinya.

A cewarsa, yan bindigan sun yi awon gaba da dabbobi da yawa.

"Sun kwashe mana shanu, tumakai, da akuyoyi da kuma kayan abinci," yace Mohammed.

Ya ce mutane sun gudu daga garin saboda tsoron dawowan yan bindigan saboda sun dade suna kai hari.

KU DUBA: Bata gari sun sake bankawa gidan jarida mallakin Tinubu, The Nation, wuta

Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 22
Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 22 Hoto: @Zamfara_state
Asali: Facebook

Tabbatar da haka, kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce "Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 20 amma ba mutane 22 ba."

Shehu ya ce yan bindigan sun kai harin ne saboda mutanen garin sun baiwa jami'an tsaro bayani kansu wanda yayi sanadiyar kisan da yawa cikinsu.

Ya ce hukumar yan sanda ta tura jami'anta damke yan bindigan.

KARANTA WANNAN: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, TVC News, wuta

A bangare guda, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa'ad Abubakar, ya alanta ranar Juma'a matsayin ranar addu'a ta musamman ga Najeriya.

Sarkin ya ce umurci Musulman Najeriya su yi addu'a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a Legas, Benin da wasu jihohi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel