Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa

- Alaafin na jihar Oyo ya cika shekaru 82 a duniya a ranar 15 Oktoban 2020.

- Matansa sun hada mishi shagalin biki tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

- Daya cikin matansa, Olori Memunat ce ta wallafa bidiyon shagalin a shafinta na Instagram

Daya daga cikin manyan sarakunan kasar nan, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya cika shekaru 82 a duniya kuma daya daga cikin matansa ta shirya masa shagali.

Baya ga murnar, matansa sun shirya masa gagarumar liyafa. Bidiyon liyafar ya karade kafafen sada zumuntar zamani.

Daya daga cikin matansa, Olori Memunat ce ta wallafa bidiyon basaraken yana rawa a liyafar.

Duk da yawan shekarunsa, babu shakka zai iya fito-na-fito da matasa wurin iya rawa.

KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa
Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Hoto daga @olori_omoh_one / IG.
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, an ga kek na liyafar tare da kyaututtuka da ya samu daga masoya. Babu shakka basaraken yayi murnar liyafar da matansa suka hada masa.

Ba a nan Olori Memunat ta tsaya ba, ta yi wata wallafa inda tayi bayanin cewa babu shakka za su iya yin komai don dauwamar da farin ciki a zuciyarsa. Ta yi wa sauran matansa jinjina.

A kalamanta: "Duk daya muke. Ba za mu iya yin komai ba amma za mu iya yin wani abu tunda Allah ya bamu iko. Ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin saka shi farin ciki. Jinjina gareku sauran sarauniyoyi."

KU KARANTA: EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

A wani labari na daban, yayin da nahiyar Afrika ta zama babban wurin shakatawa da kuma hada-hada, akwai wasu manyan filayen jiragen sama da nahiyar ke alfahari da su.

A Afrika, akwai filayen sauka da tashin jiragen sama biyar da nahiyar ke alfahari da su wurin kyau da kayatarwa, Pulse.ng ta ruwaito.

An zuba miliyoyin daloli wurin gina filayen sauka da tashin jiragen saman wanda hakan Yasa suka kasance kayatattu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel