Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya

Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bayyana illar da zanga-zangan #ENDSARS za ta yiwa da yaki da COVID-19

- Kwamtin PTF ta yi zamanta kaman yadda ta saba a ranar Litinin

- Shugaban kwamitin ya na da tabbacin yaduwar cutar cikin yan zanga-zangan

Kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, ta shiga jerin masu kira ga matasa masu zanga-zangar #ENDSARS su sassauta kuma su amince da sulhu saboda har yanzu akwai cutar Korona a gari.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hira da manema labarai a Abuja, The Sun ta nakalto

Mustafa ya siffanta masu zanga-zangan a matsayin manyan masu iya yada cutar kuma za'a fara ganin sakamakon hakan nan da makonni biyu masu zuwa.

"Maganar gaskiya itace, nan da mako biyu masu zuwa, idan ka tattara dukkan masu taro a Lekki Toll Plaza, za ka samu masu cutar da dama, " Mustafa yace.

"Duk inda mutane suka taru kuma basu bin sharrudan kariya daga cutar irinsu bada tazara, amfani da rigar rufe baki da hanci, tsafta da gudun taro, wajibi ne a yada cutar, ko ana so, ko ba'a so."

"Saboda haka ina da tabbacin cewa nan da makonni biyu, idan aka tattaro masu taro a Lekki Toll Gate da Unity Fountain dake Abuja da wuraren da ake zanga-zanga. Zamu yi fama da masu cuta da yawa nan da makonni biyu."

KU KARANTA: Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga

Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya
Boss Credit: @pulseNigeria247
Asali: Twitter

DUBA NAN: Jigo a APC, Adamu Muhammad, ya rasu

Jiya mun kawo muku cewa hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC), ta tabbatar da cewa sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba 2020.

Hukumar NCDC a shafinta na Twitter @NCDCgov, a daren ranar Litinin, ta wallafa cewa jimillar mutane 61558 ne suka kamu da cutar, yayin da mutane 56697 suka warke.

Sai dai hukumar ta wallafa cewa, mutane 1125 ne Allah ya karbi rayuwarsu sakamakon yin jinya na wannan cuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel