An sallami mutane 4,161 a rana daya yayinda sabbin mutane 113 suka kamu da cutar Korona

An sallami mutane 4,161 a rana daya yayinda sabbin mutane 113 suka kamu da cutar Korona

- Kamar yadda ta saba, hukumar NCDC ta saki adadin yan Najeriya da suka kamu da cutar Korona

- Yayinda ake samun raguwar masu kamuwa a Najeriya, maus jinya sama da 4000 sun warke a ranar Asabar

- Har yanzu kasar Rasha kadai ce ta sanar samun rigakafin cutar har guda biyu

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar COVID-19 ta sake harbin sabbin mutane 113 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:15 na daren ranar Asabar 17 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 113 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-37

Kaduna-16

Ogun-11

Plateau-11

Taraba-8

Rivers-7

FCT-6

Enugu-4

Niger-4

Edo-3

Delta-2

Imo-2

Benue-1

Kano-1

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 61,307 sai kuma mutum 56,557 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1123 suka riga mu gidan gaskiya.

A ranar Asabar kadai, an sallami mutane 4,161 dake jinya cikin gidajensu a jihar Legas bisa ga ka'idojon da NCDC ta gindaya.

An sallami mutane 4,161 a rana daya yayinda sabbin mutane 113 suka kamu da cutar Korona
An sallami mutane 4,161 a rana daya yayinda sabbin mutane 113 suka kamu da cutar Korona Hoto: NCDC
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalibi ya fille kan malaminsa saboda ya yi batanci ga manzon Allah a Faransa

Kun ji cewa cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugun cutar Korona.

Legit.ng ta tattaro cewa kwamishanan lafiyan Legas, Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar.

KARANTA: Bidiyon jami'in dan sanda rike da bindiga yana nadin tabar wiwi ya bayyana

Kwamishanan yayinda yake bayanin binciken, ya ce wata daliba mai shekara 14, yar ajin SS1 ta fara lafiya ranar 3 ga Oktoba kuma aka tura ta gida bayan karamin jinyar da tayi a makarantan.

KU KARANTA: A ceci jama'a: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel