A ceci jama'a: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro

A ceci jama'a: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro

- Aisha Buhari ta bukaci mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari, ya ceci jama'a

- Uwargidar shugaban kasa ta daura sakon haka ne a shafinta na Tuwita ranar Asabar

- A jikin sakon akwai hoton shugaban kasan da kuma waka kira ga neman dauki

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, ta daura wani gajeren sako amma mai dauke da ma'anoni da yawa a shafinta na Tuwita @aishambuhari.

Sakon da ta daura na cewa #Achechijamaa watau "A ceci jama'a"

Duk da cewa bata bayyana karara wanda take nufi da sakon ba, ta daura sakon tare da hoton mijinta, shugaba Muhammadu Buhari yana zaune da hafsoshin tsaro.

Hakazalika ta hada maganan da waka mai bukatar dauki na ceton Arewa.

KU KARANTA: Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi

Hakazalika Hajiya Aisha ta daura irin haka a shafinta na Facebook.

Wannan shine sakon na farko tun ranar Litinin da ya gabata inda ta raba sanarwan Buhari kan gyara da ake shirin yiwa hukumar SARS.

Insfekta janar na hukumar yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da rusa hukumar SARS ranar Lahadi, 11 ga Oktoba sakamakon zanga-zangan da ake yi a fadin tarayya.

A ceci jama'a: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro
Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro Credit: @aishambuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

A wani labarin, hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta tsare masu shirya zanga-zangar yunkurin kawo karshen "rashin tsaro da mulkin kwarai."

A jawabin da kakakin gamayyar kungiyoyin arewa CNG, AbdulAzeez Suleiman, ya saki ranar Asabar kuma TheCable ta samu, ya ce an tsare wasu mambobinsu da aka gayyata ofishin hukumar ta DSS domin yi musu tambayoyi amma aka tsaresu daga baya.

Ya ce wadanda aka tsare sune Nastura Sharif, Balarabe Rufai, Aminu adam da Muhammad Nawaila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel