PSC za ta kori tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki

PSC za ta kori tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki

- Akwai yiwuwar hukumar kula da 'yan sanda ta Najeriya, PSC, za ta sallami tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki

- Wannan na kunshe ne cikin shawarwarin da kwamitin shugaban kasa da aka kafa don bincike kan ayyukan rundunar SARS ta bada

- Kwamitin ta shugaban kasa kuma ta bada shawarin bincikar wasu jami'an tsohuwar rundunar ta SARS 24 da ake zargi da wasu laifuka

A kalla jami'an tsohuwar rundunar 'yan sandan masu yaki da fashi (SARS) guda 37 ne ake shirin sallama daga aiki kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ana kuma tsammanin hukumar kula da 'yan sanda, PSC, za ta bada umurnin tuhumar wasu jami'an SARS 24 da ake zargi da aikata laifuka da dama da suka saba dokar aikinsu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar aure da ɗan ta a Katsina

PSC za ta kori tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki
Jami'an 'yan sanda: Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Wadannan sune wasu daga cikin manyan abubuwan da ke cikin rahoton da kwamiti da shugaban kasa ya kafa don yi wa rundunar ta SARs garambawul a 2018 ya kunsa.

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Kwamitin ta shugaban kasa ta binciki zargin keta hakkin dan adam da amfani da karfin da doka ta bada ba bisa ka'aida ba da ake zargin wasu jami'an na SARS da aikatawa.

Da ya ke mika rahoton ga shugaban PSC, Musliu Smith a Abuja a ranar Juma'a, sakataren hukumar kiyayye hakkin dan adam, Tony Ojukwu ya bukaci a gagauta zartar da shawarwarin da kwamitin ta bayar.

Sanawar da kakakin PSC, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce Ojukwu yana kyautata tsammanin cewa shugaban na PSC zai aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton kwamitin na shugaban kasa.

Har wa yau, kwamitin ta bukaci Sufeta Janar na 'yan sanda ya bayyana sunayen jami'ai 22 da aka samu da laifin keta hakokin dan adam da cin zarafin mutanen da basu-ji-basu-gani-ba.

A wani rahoton daban, wani dan sanda da har yanzu ba a gano sunansa ba ya tsere bayan ya harbi budurwarsa a bakinta a Salvation Bus Stop da ke Ikeja a Legas. An ruwaito cewa dan sanda ya gudu ya bar budurwarsa a wurin bayan aikata laifin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel