FG ta sanar da ranar da dukkan ma'aikata za su koma aiki

FG ta sanar da ranar da dukkan ma'aikata za su koma aiki

- Gwamnatin tarayya ta bada umurnin dukkan ma'aikata manya da kanana su koma aiki ranar Litinin

- Sanarwar ta fito ne daga bakin hukumar shugaban kasa ta yaki da annobar korona, PTF, a ranar 15 ga watan Oktoba

- Amma PTF ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin FG su raba ranakun da ma'aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso

DUBA WANNAN: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

FG ta sanar da ranar da dukkan ma'aikatan ta za su koma aiki
Dakta Sanni Aliyu. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Amma a yanzu PTF ya umurci dukkan ma'aikata na ƙasa da mataki na 12 su koma bakin aiki.

Amma duk da haka ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin gwamnati su raba ranakun da ma'aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso.

A wani labarin daban, kun ji gwamnatin ta amince da bude dukkan sansanonin horas da masu yi wa kasa hidima ta NYSC a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020. Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya rubuta, "An amince da bude sansanonin horas da wadanda za su yi wa kasa hidima a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020. Za a samar da matakin dakile yaduwar Covid 19."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel