Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja

Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja

- Wasu 'yan daba dauke da makamai sun kai wa masu zanga-zangar lumana hari a Abuja

- 'Yan daban dake dauke da addunan sun ji wa masu zanga-zangar da dama raunuka

- Basu tsaya a nan ba, sai da suka lalata motoci akalla 5 dake wurin

Wasu 'yan daba dauke da makamai sun kai wa 'yan Najeriyan dake zanga-zanga akan zaluncin da 'yan sanda ke yi a Abuja hari.

'Yan daban dake dauke da adduna sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a daidai Berger, bayan kusan awa daya da fara zanga-zangar.

Sun ci mutuncin masu zanga-zangar har da masu wucewa, inda suka lalata ababen hawan dake wurin.

Sun lalata akalla motoci 5 take anan, sannan sun ji wa masu zanga-zangar munanan raunuka.

Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja
Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: 'Yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da fashi a cikin cunkoso a Legas

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Wadanda ke rundunar daga arewaci da kuma kudu maso yamma za a horar da su a kwalejin horar da 'yan sanda da ke Nasarawa da ta Ila-Orangun, jihar osun.

Takardar ta kara da bayyana cewa, umarni daga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya shine dukkan jami'an SARS su bayyana a hedkwatar 'yan sanda da ke Abuja domin gwajin lafiya da kwakwalwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel