Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari

Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai

- Ganduje ya dakatar da kakakinsa ne bayan ya soki Shugaba Muhammadu Buhari game da zanga-zangan neman soke 'yan sandan SARS da al'umma suka yi

- Yakasai ya nuna takaicinsa kan abinda ya kira rashin tausayi da halin ko-in-kula da Shugaba Buhari ke nuna wa 'yan Najeriya

Yanzu-yanzu: Ganduje ya dakatar da kakakinsa, Salihu Tanko, saboda sukar Buhari
Gwamna Abdullahi Ganduje da Tanko Yakasai. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.'

Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.

DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

Ya ce duk da cewa hadimin gwamnan yana da ikon yin tsokaci kan batutuwa don ra'ayinsa, a matsayinsa na mutum mai rike da mukami, yana da wahalar a banbance ra'ayinsa da matsayin gwamnan a kan batutuwa da suka shafi al'umma.

Gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati su kiyayye yin maganganu da ka iya tada zaune tsaye da janyo cece-kuce.

Tunda farko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ban taba ganin gwamnati mara tausayi ba kamar irin ta Buhari. Lokuta da yawa mutane suna shiga mawuyacin hali kuma suna bukatar ya basu kwarin gwiwa cewa yana daukan matakai a kai amma baya yin hakan. Halin ko-in-kula da ya ke dashi na daban ne."

KU KARANTA: Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

A wani rubutun da ya wallafa a Twitter: "Yi wa al'ummar ka magana kan abubuwan da ke damunsu ya zama tamkar alfarma ka ke musu. Ka gaza ware ko da minti biyar ka kwantar wa mutane hankali, mutanen da ka bi jihohi 36 ka nemi kuri'arsu, abin takaici ne wannan."

A wani labarin daban, ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa - Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel