Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke rundunar SARS a jihohi 36 na kasar da Abuja

- An soke rundunar biyo bayan zanga-zanga da al'umma suka rika yi a tituna da dandalin sada zumunta a kasar

- Rundunar 'yan sandan ta ce za a sauya wa 'yan sandan da ke tsohuwar rundunar ta SARS wuraren aiki nan take

Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.

Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan.

Wannan na dauke ne cikin wata jawabi da ya yi kai tsaye a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoban 2020.

Yanzu-yanzu: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya
Mohammed Adamu: Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47

Sanarwar na zuwa ne bayan al'umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna da kuma dandalin sada zumunta na neman a soke rundunar a kasar baki daya don kisa da cin zarafin al'ummma da suke yi.

Yayin jawabin, IGP ya ce, "An soke Rundunar tarayya ta musamman masu yaki da fashi da makami da aka fi sani da SARS a dukkan rundunonin 'yan sanda da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja."

KU KARANTA: Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

Bayan jawabin, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa DCP Frank Mba ya fitar da wata sanarwa mai taken, 'IGP ya soke rundunar ta musamman mai yaki da fashi da aka fi sani da (SARS)', wani sashi na cikin sanarwar ya ce:

"Bisa la'akari da kiraye-kirayen da 'yan Najeriya suka yi, za a tura jami'an tsohuwar rundunar ta SARS da aka rushe zuwa wasu sassa karkashin rundunar 'yan sandan nan take.

"IGP din ya ce ta rundunar ta san cewa akwai bukatar ayi yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka da ke karuwa a kasar da a baya rundunar ta SARS ke yi."

A wani labarin daban, Ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa - Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel