Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe

Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe

- Jama'a sun dinga neman inda za su boye domin ceton rayukansu a wurin tattar sakamakon zabe

- Hakan ta faru ne sakamakon musayar ruwan wuta da ake yi tsakanin 'yan sanda da 'yan daba

- An ji 'yan sandan suna shawarta jama'a da su san inda dare yayi musu sannan suna kokarin bai wa wurin tattara sakamakon kariya

Manema labarai, wakilan jam'iyyu da kuma masu lura da zabe sun tarwatse inda suka dinga neman maboya sakamakon ruwan wutar da ake musaya tsakanin 'yan sanda da 'yan daba.

Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St Peter da ke Akure a ranar Asabar.

Ana amfani da makarantar firamaren wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo.

Jami'an hukumar zabe suna ta hada-hada domin fara tattara sakamakon zabe a lokacin da rikicin ya barke.

"Ku bar nan, ku tafi! Bai kamata ku tsaya ba," wasu 'yan sanda ke sanar da hakan ga manema labarai da masu lura da zabe yayin da suke mamaye kofar shiga wurin tattara sakamakon.

KU KARANTA: Da duminsa: Harbe-harbe ya barke a wata rumfar zabe a Ondo

Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe
Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

Karin bayani yana nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel