Korar jami'an Immigration 60: Har shiga irin ta masu aikin shara na yi don kama masu cin hanci - Babandede

Korar jami'an Immigration 60: Har shiga irin ta masu aikin shara na yi don kama masu cin hanci - Babandede

- Hukumar Kwastam ta sallami jami'anta 60 daga aiki a cikin shekaru hudu da suka gabata

- Shugaban Hukumar, Mohammed Babandede ya ce akwai lokutan da ya yi shiga irin ta mai shara don kama jami'ai masu karɓar rashawa

- Babandede ya ce hukumar tana gudanar da sahihin bincike kafin daukan matakin korar jami'ai da ake zargi da cin hanci

Hukumar Kula da Shiga da Fice ta Ƙasa ta ce ta kori jami'anta 60 bayan an kama su suna karɓa ko bada toshiyar baki.

Shugaban hukumar, Muhammad Babandede ne ya sanar da hakan a hirar sa da BBC Hausa a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

Ya kuma ce ya taɓa yin ɓadda-kama a matsayin mai shara domin ya cafke masu karɓar toshiyar baki.

Hukumar Immigration ta kori jami'anta 60 daga aiki
Muhammad Babandede. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

Babandede ya ce an kori jami'an 60 ne cikin shekaru hudu da suka shude bayan anyi ƙarar su "tare da hujjoji" da aka gabatar wa hukumar ta hannun Ma'aikatan Harkokin Cikin Gida.

"Kimanin shekaru hudu kenan da muka hana bada toshiyar baki don tura jami'ai wuraren ayyuka masu kyau kamar yadda aka saba a baya. Ƙarƙashin Ma'aikatar Cikin Gida, Mun sallami jami'ai 60 da aka kama da laifin rashawa a filayen jiragen sama da toshoshin ruwa," in ji shi.

"Akwai gurɓatattun jami'ai har cikin manya. Amma hakkin mu ne a matsayin shugabanni mu hana hakan musamman batun bada cin hanci don tura jami'ai boda da tashoshin jiragen ruwa. Mun kuma hana jam'i a da ke aiki a wuraren kai wa manyan su kudi. Duk wanda aka kama zai gane kurensa.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

"Hukumar Immigration ta shirya don yaƙi da rashawa. Na taɓa yin shiga irin ta masu shara a filin tashin jiragen sama da tashan jirgin ruwa don in kama gurɓatattun jami'ai. Ba zamu iya aikin mu kadai ba musamman yanzu da sauran hukumomin tsaro ke taya mu tsare iyakokin ƙasa," in ji Babandede.

Har wa yau, ya ce dole duk wata hujja da za a gabatar game da jam'in da ake zargi da karɓa ko bada rashawa ya zama sahihi.

A wani labarin, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel