Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah

Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah

- Kusan mako daya yanzu da bada iznin cigaba da Umrah, babu wanda ya kamu da Korona

- An tanadarwa tsofaffi da marasa karfi hanyoyi na musamman domin nasu ibadar

- Saudiya ta samu saukin sabbin masu kamuwa da Korona yayinda masu waraka na kara yawa

Akalla mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah tun lokacin da aka bude Mallacin Harama dake Makkah ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, 2020 kuma babu wanda ya kamu da cutar Korona.

Ofishin kula da lamuran Masallatan harama biyu a ranar Laraba ta ce an samar da ka'idoji domin kare maniyyata da kuma hana yaduwar cutar COVID-19.

"Matakan kariyan da muka shirya domin Umarah lokacin Korona sun hada da tsaftace muhalli, hana cakuduwan da jama'a da kuma wayar da kan mutane, " Kakakin ofishin, Hani Haidar.

"Mun shirya cibiyoyin kebance duk wanda aka gani da wasu alamun cutar."

"Amma babu labarin wanda ya kamu da COVID-19 ko daya har yanzu."

Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah
Credit: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

Domin tabbatar da cewa ana baiwa juna tazara, ofishin ta shirya hanya ta musamman ga masu manyan shekaru da kuma masu nakasa saboda su gudanar da Umrah cikin kwanciyan hankali.

Haidar yace ma'aikata 4000 aka tanada domin tsaftace Masallacin Ka'aba akalla sau 10 a rana.

Hakazalika an tanadi litan sinadarin tsaftace muhalli saman da lita 1,8000 domin wanke bayan gida sau shida a rana.

Bugu da kari, ana goge na'urar bada sanyi watau AC akalla sau tara a rana.

DUBA NAN: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

A wani labarin daban, Wata kotu a kasar Yemen ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutum 10 ciki har da Shugaba Donald Trump, Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Yarima Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud saboda aikata laifukan yaki.

An zartar da hukuncin ne a wani Kotu na musamman na masu manyan laifuka a Saada akan harin hadin gwiwa da aka kai wa wata motar bas cike da kananan yara a mazabar Majz.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel