An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu

An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu

- An gano wani lauyan bogi a yayin da ya tafi kotu domin kare wani mutum a jihar Ogun

- Alkalin kotun bai gamsu da wasu abubuwa da lauyan ya yi bane yasa ya tambaye shi shekarar da ya samu izinin fara aikin lauya

- Da ya bincika bai ga sunan lauyan bogin ba hakan yasa ya kira 'yan sanda suka tisa keyarsa zuwa caji ofis

'Yan sandan jihar Ogun sun kama wani lauyan bogi Tajudeen Idris mai shekaru 47 kan zarginsa da yin soja gona.

An kama wanda ake zargin ne a ranar Juma'a a kotun Majistare ta 6 da ke karamar hukumar Ifo na jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Matsalolin Najeriya: Rashin tunani zai sa a dora wa mulkin soja laifi - Babangida

An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu
An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

An ruwaito cewa Idris ya hallarci kotun ne gaban mai shari'a I.A. Arogundade domin kare wani Ifeanyi Chukwu da ke shari'a da Ayo Itori.

Ya yi ikirarin cewa shi lauya ne da ke aiki da Tajudeen O. Idris & Co. Chambers kuma ya hallarci kotun ne don kare daya daga cikin wadanda ake yin shari'a da shi.

Kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

KARANTA NAN: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

Oyeyemi ya ce yanayin yadda lauyan bogin ya gabatar da kansa a kotun ne yasa aka fara zargin ko tabbas shi lauya ne.

Hakan yasa alkalin kotun ya tambaye shi shekarar da ya samu izinin fara aiki a matsayin lauya kuma ya ce 2009.

"Amma binciken da aka yi ya nuna babu sunansa cikin wadanda suka samu izinin aikin lauya a shekarar 2009 hakan yasa aka gayyaci 'yan sanda.

"DPO na 'yan sanda na yankin Ifo, CSP Adeniyi Adekunle ya tura jami'ansa suka kama wanda ake zargin inda yanzu ake cigaba da bincike a kan lamarin." inji shi.

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel