ISWAP ta sako manyan jami'an jihar Borno 5 da ta yi garkuwa da su

ISWAP ta sako manyan jami'an jihar Borno 5 da ta yi garkuwa da su

- Mayakan ta'addancin ISWAP sun sako jami'an jihar Borno biyar

- An sace manyan ma'aikata a watan Augustan da ta gabata

- Gidauniyar Umul-Kulthum ce ta cetosu da hadin guiwar 'yan uwansu

An ceto ma'aikatan gwamnatin jihar Borno 5 da 'yan kungiyar ISWAP sukayi garkuwa dasu watan da ya gabata.

Anyi garkuwa da ma'aikatan RRR dinne, yayin da suke kan hanya tsakanin Maiduguri da Monguno.

Ma'aikatan 5 sun bayyana a wani bidiyo ne jiya suna neman taimakon gwamnatin jihar Borno.

'Yan ta'addan sun yi ikirarin kai wa ma'aikatan gwamnati farmaki akan aikin da suke yi wa "makiya addinin musulinci."

'Yan ta'addan sun yi ikirarin hakan kafin su kai wa ma'aikatan farmaki, inda suka kama wasu ma'aikatan tsaro a watan Ogusta.

"Da farko anyi tunanin ba ma'aikatan gwamnati bane," kamar yadda labarin yazo.

"Amma sai suka canja ra'ayinsu da suka gano cewa kananan ma'aikatan RRR suka kama, mafi yawa ma leburori ne," gidauniyar tace.

KU KARANTA: Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo

Jaridar Premium Times tace da taimakon Umul-Kalthum Abdurrahman, shugaban wata gidauniya ta KFP aka samu suka sako ma'aikatan.

A wata hira da Premium Times tayi da Ummu-kalthum, ta tabbatar da cewa gwamnati da kuma 'yan uwan wadanda aka yi garkuwa dasu ne suka tuntube ta, inda ta tsaya tsayin-daka domin ganin ta fitar da ma'aikatan ba tare da an basu ko sisi ba.

ISWAP ta sako manyan jami'an jihar Borno 5 da ta yi garkuwa da su
ISWAP ta sako manyan jami'an jihar Borno 5 da ta yi garkuwa da su. Hoto daga @PremiumTimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya

Tace, "Abinda na sani shine, gwamnati da 'yan uwan wadanda aka kama sun tuntubemu sakamakon taimakon ceto mutane da dama da suka samu labarin munyi, daga hannun 'yan ta'addan.

"Mun samu tattaunawa da 'yan ta'addan ta wasu lambobi, inda suka ce zasu kashe su in dai bamu yi wani abu ba da wuri. Sai suka ce zasu bada kwanaki zasu yi rangwame na 'yan kwanaki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel