Na kama matata ta na cin amanata da magidanci a gadonmu na aure - Tsohon minista Femi Kayode
- Bayyanar faifan bidiyon tsohon minista Femi Fani Kayode (FFK) ya na zazzagawa tsohuwar matarsa masifa sun haddasa cece-kuce a dandalin sada zumunta
- Har yanzu FFK bai saki matarsa ta hudu ba duk da sun dade basa zaune tare sakamakon rikicin 'da ya ki ci, ya ki cinyewa' a tsakaninsu
- Ana yawan zargin FFK tare da sukarsa a kan rashin hakuri da mata
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya magantu a kan wani faifan bidiyo da ke nuna shi ya na zazzagawa matarsa da su ka rabu, Precious Chikwendu, masifa.
FFK ya garzaya shafinsa na Instagram domin kare kansa a yayin da wasu kafafen yada labarai da ma'abota dandalin sada zumunta ke caccakarsa a kan rashin hakuri da mata.
A cewar tsohon ministan; "SaharaReporters ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna ni a matsayin mai cin zarafin matarsa.
DUBA WANNAN: Kawatace kawai - Tsohon minista Fani Kayode ya yi magana a kan hotunansa da Halima Yusuf
"Wannan ba wani abu bane face yada farfaganda da son batamin suna.
"Babu wani abu a faifan bidiyon sai kokarin da na ke yi na son karbe wayarta ta hannu domin hanata nadar sabanin da muka samu.
"Babu inda aka ganni ina cin zarafinta a faifan bidiyon, hatta fadan da na ke yi saboda na kamata ta na cin amanata da wani mutum mai aure ne.
DUBA WANNAN: Najeriya @60: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta
"Na kara maimaita cewa ban ci zarafinta ba, ita ce ta ke cin zarafin jama'a, halinta ne cin zarafin jama'a tare da wulalantasu kamar yadda ta ke yi wa 'yan uwana, ma'aikatana, kananan yara da leburorin da ke aiki gidanmu.
"Za a iya sauraron kalamaina a faifan bidiyon, na fada ma ta cewa kowa zaman lafiya ya ke so amma banda ita. Ban taba cin zarafinta ba duk da na kamata da kwarto," a cewar FFK.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng