Sabbin mutane 160 sun kamu da Korona, yayinda ake gab da isa 60,000
Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Juma'a 3 ga watan Oktoba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Rivers-42
Lagos-32
Plateau-21
FCT-18
Kaduna-14
Ogun-11
Katsina-10
Kwara-3
Ondo-3
Imo-3
Anambra-1
Abia-1
Oyo-1
Jimillan wadanda suka kamu: 59,287
Jimillan wadanda aka sallama: 50,718
Adadin wadanda suka yi wafati: 1,113
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng