Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda zai magance kallubalen tsaro musamman a Arewa maso Yamma

- Tambuwal ya bawa Buhari shawara ya samar wa hukumomin tsaro fasahar sadarwa ta zamani wato ICT don taimaka musu wurin aikinsu

- Gwamnan ya kuma shawarci shugaban kasar ya dauki matasa ayyukan hukumomin tsaro duba da cewa akwai karancin jami'an tsaro a kasar

Shugaban kungiyar gwamnoni na jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da fasahar sadarwar zamani, ICT, don magance kallubalen tsaro musamman a Arewa maso Yamma.

Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari
Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari. Hoto: @DailyPostNGR
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da 'yan jarida lokacin da shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya jagoranci wata tawaga zuwa jihar Bauchi don kaiwa gwamnan ziyara a ranar Juma'a.

Tambuwal ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma inda ya ce akwai karancin 'yan sanda ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matasan da suka cancanta aiki a hukumomin tsaro.

Ya ce, "Ina kira ga shugaban kasa ya duba yiwuwar daukan matasa da suka cancanta aiki. Muna da matasa da dama masu kishin kasa marasa aikin yi da za su iya shiga aiki irin na 'yan sanda, Soji, DSS da sauran hukumomi.

KU KARANTA: Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden

"Ina kira ga Shugaban kasa ya duba yiwuwar daukan wadannan matasan da suka cancanta domin mun san akwai karancin jami'an tsaro a Najeriya, akwai bukatar kari. Na san muna kokari kan batun 'yan sandan unguwa amma hakan ba zai wadatar ba.

"Kazalika, muna kira ga Shugaban kasa ya samar da fasahar sadarwar zamani wato ICT ga dakarun mu da ke yaki da ta'addanci, 'yan bindiga, masu garkuwa da sauran laifuka."

Sauran wadanda ke tawagar sun hada da Secondus, mataimakin shugaban PDP na kasa shiyyar Arewa, Nazif Gamawa, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo.

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel