Da yiwuwan PPMC ta rage farashin man fetur wannan watan

Da yiwuwan PPMC ta rage farashin man fetur wannan watan

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta cire hannunta daga tsarin rage ko kara farashin mai

- Shugaba Buhari ya ce sam ba zai sake biyan tallafin mai ba

- Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce hakan ne daidai ga Najeriya

Kamfanin kasuwancin kayayyakin arzikin man fetur PPMC na iya rage farashin man fetur wannan watan, The Nation ta ruwaito.

A hira da mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandu, ya bayyana cewa yan kasuwan na kyautata zaton za'a rage farashin man a watan Oktoba.

Ya bayyana hasashensa ne bisa ga saukar farashin mai a kasuwar duniya. Farashin yanzu ya sauko $39.38.

Amma ya ce sai kamfanin PPMC ta sanar da sabon farashin zasu fara sayarwa.

Amma hukumar lura da farashin man fetur PPPRA a watan Satumba ta ce ba farashin mai a kasuwar duniya kadai za'a duba wajen rage ko kara farashin a nan gida ba.

Zaku tuna cewa gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai a watan Maris na shekaran nan.

A watan Satumba, PPMC ta sanar da farashin man fetur da za'a sayarwa yan kasuwan mai a N151.56 ga lita, amma ta ki fadin farashin da su yan kasuwan zasu sayarwa yan Najeriya.

Saboda haka, yan kasuwan a fadin tarayya suka fara sayar da man tsakanin N158 da N162 ga lita.

DUBA NAN: Yan fashi sun kai farmaki banki, sun yi awon gaba da makudan kudi

Da yiwuwan PPMC ta rage farashin man fetur wannan watan
Da yiwuwan PPMC ta rage farashin man fetur wannan watan
Asali: UGC

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya na ganin cewa babu hikima ace Najeriya ta na saida man fetur kasa da abin da ake saidawa kasashen da ke makwabtaka.

Mai girma shugaban kasar ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.

Buhari ya ce ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da rike farashin fetur ba saboda halin da ake ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel