Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa

Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa

- Mataimakin gwamnan Sokoto Alhaji Munnir ya yi karin haske game da ginin tagwayen titi da ake yi zuwa fadar mahaifinsa, Sarkin Yamman Kware, Muhammad Dan'iya

- Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin jihar da ta gabata ne ta bada aikin ginin titin tun kafin a nada mahaifinsa hakimi

- Ya ce aikin na cikin kwangilar ginin titi mai tsawon kilimita 5 da gwamnatin ta bada a kananan hukumomi 23 na jihar

Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa
Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Munnir Dan'iya ya kare kansa game da aikin ginin titi mai tsawon kilomita 1.530 da ake gina wa zuwa fadar sarkin Yamman Kware, Alhaji Muhammad Dan'iya.

Alhaji Muhammadu Dan'iya, wanda shine mahaifin mataimakin gwamnan yana daya daga cikin sabbin hakiman da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nada kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya

Rahotanni sun ce ma'aikatar kananan hukumomi da ayyukan cigaba wadda mataimakin gwamnan ke shugabanta ce ta bada kwangilan ginin titin.

Amma kakakin mataimakin gwamnan, Aminu Abdullahi Abubakar ya yi bayanin cewa an bada kwangilar ginin titin tun kafin a nada mahafin mataimakin gwamnan a matsayin hakimi.

Ya ce aikin na cikin kwangilar gina titi mai tsawon kilomita biyar cikin kananan hukumomi 23 da gwamnatin jihar da ta gabata ta bayar saboda haka ba son kai bane yasa aka kirkiri aikin.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, na kasa Farfesa Tunde Adeniran a ranar Talata ya sanar da cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa ta hammaya.

Adeniran ya sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannunsa da kwanan watan 29 ga watan Satumban 2020 da ya aike wa hedkwatan jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel