Kundin Tarihi: Jerin abubuwa masu muhimmanci 20 da suka faru daga 1960 zuwa 2020

Kundin Tarihi: Jerin abubuwa masu muhimmanci 20 da suka faru daga 1960 zuwa 2020

Shekaru 60 yau da samun yancin Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka a 1960.

Ga jerin muhimman abubuwa 20 da suka faru cikin shekarun nan da Legit.ng ta kawo muku:

20. Daga samun yanci aka nada shugabannin kasar kuma Abubakar Tafawa Balewa ya zama Firai Minista

19. A 1963, Najeriya ta zama jamhuriyya. Nnamdi Azikwe ya zama shugaban kasar na farko

18. A 1966, Sojoji Inyamurai sukayi juyin mulkin farko a watan Junairu inda aka kashe manyan Arewa irinsu Tafawa Balewa, Ahmadu Bello Sardauna, dss.

17. Manjo Janar Aguiyi Ironsi ya zama shugaban kasar mulkin Soja na farko

16. Sojoji yan Arewa suka dau fansa inda suka yi wani juyin mulkin a Yulin 1966. Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa kuma ya samar da jihohi 12 maimakon yankuna 4 da ake da su

15. Laftanan Kanar Ojukwu ya sanar da ballewar yankin inyamurai a 1967 kuma ya sanyawa kasar suna Biyafara. Hakan ya haifar da yakin basasa tsakanin 1967 da 1970. Kimanin mutane milyan daya aka kashe.

14. A 1975, Birgediya Janar Murtala Mohammed, ya yiwa Yakubu Gowon juyin mulki. Murtala ta samar da sabbin jihohi 7.

13. An kashe Murtala a 1976 kuma Obasanjo ya zama shugaban kasa kuma ya mayar da kasar mulkin demokradiyya inda a shirya zabe a 1979.

12. Shehu Shagari na jam'iyyar National Party of Nigeria NPN ya lashe zaben a 1979 kuma ya sake lashewa a 1983.

11. A 1983 aka sake wata sabuwar juyin mulki inda Manjo Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa

10. Saboda tsananin da ake ganin Buhari na yi na yaki da rashawa da barayin gwamnati, an yi masa juyin mulki kuma Ibrahim Babangida ya zama shugaban kasa.

09. Babangida ya yi yunkurin mayar da mulki hannun farin hula a 1992 amma ya soke zaben shugaban kasan da ya shirya a 1993 bayan ya bayyana karara cewa dan kasuwa, Moshood Abiola, ne zai lashe zaben.

08. Bayan haka aka nada Ernest Shonekan shugaban kasan rikon kwarya a a Nuwamban 1992, Abacha yayi masa juyin mulki. Ya sa aka daure Abiola har mutuwarsa a Yulin 1998.

07. Bayan shekaru biyar a mulki, Abacha ya mutu a shekarar 1998

06. Shugaban hafsoshin tsaro na lokacin, AbdulSalami Abubakar ya zama shugaban kasan rikon kwarya.

05. AbdulSalami Abubakar samar da hukumar gudanar da zabe NEC a Agustan 1998

04. AbdulSalami ya mayar da mulki hannun farin hula a 1999. Ya sake mutane tara da Abacha ya daure, har da Obasanjo. A zaben da ya shirya, Olusegin Obasanjo na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya lallasa Olu Falae.

03. Kafin saukar AbdulSalam daga mulki, ya samarda kundin tsarin mulkin Najeriya a 1999.

02. PDP ta jagorancin Najeriya na tsawon shekaru 16 karkashin Obasanjo, Umaru Yar'adua, da Goodluck Jonathan.

01. A 2015, Muhammadu Buhari na jam'iyar APC ya kada shugaban dake kai, Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel