Makarantun FGC zasu iya komawa karatu- Adamu Adamu

Makarantun FGC zasu iya komawa karatu- Adamu Adamu

- Zaman gida ya kare, makarantun tarayya sun fara komawa karatu bayan watanni 6 a gida

- An bayyanawa daliban makarantun kwana ranar da zasu koma

- Gwamnatin jihar Yobe ce ta kusa-kusa wajen sanar da ranar komawa makaranta

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya sanar da ranar bude makarantun tarayya a fadin kasar.

Za'a bude makarantun ranar 11 ga watan Octoba, 2020.

Wannan na kunshe na a wata wasika da Ministan ya rattaba hannu a ranar Laraba a garin legas.

Sai dai bude makarantun zai shafi dalibai yan makarantar sakandare ne kawai.

DUBA NAN: Najeriya @60: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta

Makarantun FGC zasu iya komawa karatu- Adamu Adamu
Makarantun FGC zasu iya komawa karatu- Adamu Adamu
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

Adamu yace anyi hakane domin aba daliban da suka dade zaune a gida damar kammala zangon karantunsu wanda zai kare karshen disamba.

Ministan ya bada shawara akan abi ka'idojin kare kai daga cutar Covid-19 a makarantun domin takaita yaduwar ta tsakanin dalibai.

"Har ila yau, Makarantun da basu kammala zangon karantunsu na biyu ba suyi kokari su kammala sannan su shiga zangon karatu na uku wanda ake sa ran zai kare a watan disambar 2020, "A cewar shi.

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni da gwamnoni 'yan uwansa sun jawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum kunne akan ya dinga tsananta tsaro musamman idan zai je wurare masu hadarin gaske, amma sai yace "ya batun mutane na na jihar Borno? Me zai faru dasu?" A wannan halin tashin hankalin dake Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel