Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait

Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait

- Bayan rasuwar tsohon sarki Sheikh Sabah, Kuwait ta samu sabon sarki

- An tattaro cewa Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Sarki

- Sheikh Nawaf ya sha alwashin yin aiki domin samar da daidaito da tsaro a Kuwait

Rahotanni sun kawo cewa an nada Sabon Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah. Tuni dai sabon sarkin ya karbi rantsuwar kama aiki.

Wannan ci gaban na zuwa ne kwana daya bayan sanar da rasuwar tsohon Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah.

KU KARANTA KUMA: Sabon rahoto: Ministan ƙwadago ya faɗi lokacin da ASUU za ta janye yajin aikin da ta shiga

Sheikh Nawaf, wanda shi ne yarima mai jiran gado a baya, ya dauki alkawarin yin aiki domin samar da daidaito da tabbatar da tsaro a Kuwait.

Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait
Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Ba a tsammanin Sheikh Nawaf mai shekara 83 zai kawar da kasar daga manufofin cikin gida da na ƙasashen duniya da magabacinsa kuma dan uwansa ya samar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu (Sunaye da jihohi)

A baya, mun kawo cewa Sarkin Kuwait mai shekaru 91 da haihuwa, Sarki Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu ranar Talata a wani asibiti a Amurika.

"Muna bakin cikin sanar da mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-jaber Al-Sabah, sarkin Kuwait," inji Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah, ministan yada labaran kasar.

An haifi Sheikh Sabah a shekarar 1929, ya rike kujerar ministan harkokin kasashen waje na tsawon shekaru 40, tsakanin 1963 zuwa 2003 daganan ya zama shugaban kasa.

Ya zama sarkin Kuwait a watan Janairu, 2006 bayan rasuwar Sheikh Jabeer Al-Sabah.

A watan Augusta 2019 an sanar da rashin lafiyarsa duk da ba'a fadi cutar da ke damunsa ba, har ta kai ga an kwantar da shi a asibiti.

An fitar dashi Amurka don duba lafiyarsa a watan Yulin 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel