Sayar da NNPC zamu yi ba shafeta ba - Ministan Mai

Sayar da NNPC zamu yi ba shafeta ba - Ministan Mai

- Karamin Ministan kudi ya yiwa yan Najeriya bayanin sauyin da Gwamnatin Buhari ke shirin yi wa NNPC

-Ya yi kira ga yan Najeriya suyi watsi da jita-jitan da ake cewa za a shafe hukumar

Karamin ministan man fetur, Temipre Sylva, ya yi fashin bakin kan lamarin dake tattare da dokar sauye-sauye a cikin kamfanin man feturin kasa watau NNPC da ya aikewa majalisar dokokin tarayya.

Ministan ya bayana cewa ba shafe kamfanin NNPC za’ayi ba, face sayar da ita kawai.

Ya bayyana hakan ne yayında yaka hira da manema labarai ranar Litinin bayan ganawarsa da shugabannin majalisar dokokin tarayya.

Mun ji maganganu iri-iri kan cewa za’a shafe NNPC amma babu abu mai kama da hakan cikin abinda muka gabatar. Ba za’a staffe NNPC ba amma za’a sayar da ita bisa ga sharrudan sauye-sauyen da aka aiwatar kan dukkan rasen man fetur a kasar nan, “ Yace

Jaridar Punch ta samu bayanai abubuwa da dokar ta kunsa kamar da yadda Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

Dokar na bukatar duba irin canje-canjen da za’a iya yiwa NNPC da PPPRA. Hakazalika dokar na bada shawarar kirkirar sabuwar kamfani mai suna Kamfanin Man Feturin Najeriya.

A ganawar da shugabannin majalisar dattawa, Minista Sylva ya jaddada muhimmancin tabbatar da dokar cikin karamin lokaci saboda a samu masu sana hannun jari nan da 2040.

A bangaren majalisar, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya tashi takobin kafa tarihi ta hanyar tabbatar da cewa dokar ta samu gin din zama.

KU KARANTA: Ana saura kwanaki 11 zabe, Buhari na son baiwa jihar Ondo N7bn

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ga majalisar dokokin tarayya makon gobe, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya laburta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel