Dalilanmu na jingine yajin aiki - Kungiyar Kwadago ta magantu

Dalilanmu na jingine yajin aiki - Kungiyar Kwadago ta magantu

- A ranar Litinin din da ta gabata ne kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi niyyar shiga yajin aikin karin farashin mai da na wutar lantarki

- Sai dai, daga bisani, NLC ta sanar da janye shiga yajin aikin bayan kammala wata ganawa da gwamnatin tarayya da tsakar daren ranar Litinin

- Janye yajin aikin da NLC ta yi ya fusata wasu 'yan Najeriya tare da zargin kungiyar da sayar da jama'a a hannun shugabanni

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da aminiyarta ta 'yan kasuwa (TUC) sun bayar da dalilansu na fasa shiga yajin aiki da zanga-zangar da su ka yi niyya.

NLC da TUC sun bayyana dalilansu ne a cikin wata sanarwa ta hadin gwuiwa da su ka fitar ranar Talata.

Takardar na dauke da sa hannun shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba, shugaban TUC, Quadri Olaleye, sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, sakataren TUC, Musa Lawal Ozigi, shugaban NUPENG, Williams Akporeha, shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, shugaban NUEE, Martin Uzoegwu, da shugaban SSAEAC, Chris N. Okonkwo.

A cewar shugabannin kungiyoyin, sun yi la'akari da tasirin annobar korona a rayuwar 'yan Najeriya kafin su yarda su jingine yajin aikin.

KARANTA: Ba gudu, ba ja da baya: NLC ta lissafa sharudan fasa shiga yajin aiki

Sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi mu su bayani mai gamsarwa a kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki da dalilan kara kudin wutar lantarki da kuma kara farashin man fetur.

Kungiyoyin sun bayyana cewa Najeriya da sauran kasashen duniya sun shiga mawuyacin halin tattalin arziki sakamakon bullar annobar korona.

Dalilanmu na jingine yajin aiki - Kungiyar Kwadago ta magantu
Zamnan tattaunawar NLC da shugabancin majalisa
Asali: UGC

A cewar kungiyoyin, yanzu ne lokacin da kasashen duniya ke daukan sabbin matakan farfado da tattalin arzikinsu bayan lafawar annobar korona.

KARANTA: Kano: Kotu ta zartar da hukuncin daurin wata 7 a kan mashayin tabar wiwi

Batun janye yajin aikin NLC ya fusata 'yan Najeriya da dama tare da yi wa kungiyar zargin cewa ta yaudari jama'a tare da sayar dasu a wurin shugabanni.

A ranar Litinin, 26 ga watan Satumba, kungiyar NLC ta yi niyyar shiga yajin aiki tare da fara zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur da na kudin wutar lantarki.

Sai dai, kungiyar ta fitar da sanarwar janye shiga yajin aikin da ta yi niyya bayan kammala wata ganawa da gwamnatin tarayya da tsakar daren ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel