Shugaba Buhari zai gabatar da Kasafin kudin 2021 mako mai zuwa - Shugaban majalisar dattawa

Shugaba Buhari zai gabatar da Kasafin kudin 2021 mako mai zuwa - Shugaban majalisar dattawa

- Kamar yadda ya saba, shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana gaban yan majalisa

- Wannan karon, ba zai fuskanci matsala ba kamar yadda yayi bara

- Sh majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya sanar da hakan

Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ga majalisar dokokin tarayya makon gobe, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya laburta.

Ya bayyana hakan cikin jawabin maraba da zuwan da yayiwa Sanatoci bayan watanni da suka kwashe suna hutu.

Yan majalisan sun koma bakin aiki ne ranar Talata amma suka shiga ganawar sirri na tsawon kimanin mintuna 90.

Yayin jawabi ga Sanatocin, Ahmad Lawan ya jinjinawa kwamitin hadaka na mambobin kwamitin Audi na majalisar da kuma ma’aikatar kasafin kudi don shirya takardar yadda za’ayi gudanar da MTEF.

KU KARANTA: Sayar da NNPC zamu yi ba shafeta ba - Ministan Mai

Kwamitin ta tattauna da sama da ma’aikatun gwamnati 300 kan lamuran samar da kudin shiga da kuma shigar da kudin da aka samu asusun gwamnatin tarayya,” Yace.

“Kwamitin Hamadan sun gabatar da rahotonsu ga majalisar dattawa yau domin dubawa da tabbatarwa. Wannan shine matakin farko na gabatar da kasasın kudin 2021 da majalisar zartaswa zatayi nan ba da dadewa ba.”

“Na samu labarin cewa majalisar zartaswa za ta gabatar da kasa fin kudin 2021 makon gobe.”

Majalisar dattawa, a cewarsa, za ta bada wata daya domin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su bayyana gabanta domin yin bayanin yadda zasu kashe kudaden da suka bukata a kasafin kudin.

Kaman yadda akayı a bara, za’ayi amfani da watan Oktoba wajen sauraron bayanan ma'aikatu.

Sauran watannin Nuwamba da Disamba kuma, yan masjalisa zasu yi amfani dasu wajen duba abubuwan da ke ciki.

KU KARANTA: Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin tarayya ta bash damar baiwa jihar Ondo, Bayelsa,Cross River, Osun da Rivers, kudi N148bn kan wasu gine-ginen titunan gwamnatin tarayya da suka yi.

Shugaban kasan ya gabatar da bukatarsa ne ta wasikar da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, kuma aka karanta a zauren masjalisa radar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel