Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC

Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC

- Ministar tallafi da jin kan 'yan kasa ta barranta ma'aikatarta da damfarar da ICPC ke zargi

- Sadiya Farouq ta ce ba dai daga ma'aikatarta aka bankado kwashe kudi har N2.67 na abinci ba

- Ministar ta ce ma'aikatarta tana ciyar da yara 'yan aji daya zuwa uku ne ba 'yan kwaleji ba

Sadiya Umar Farouq ta ce ma'aikatar tallafi da jin kai bata da alaka da damfarar N2.67 biliyan na ciyar da 'yan makaranta, wacce hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta bankado.

A ranar Litinin, ICPC ta sanar da cewa an bankado wasu N2.67 biliyan wacce gwamnatin tarayya ta biya domin ciyar da 'yan makaranta, a wasu asusun bankuna masu zaman kansu.

Amma a wata takarda da Nneka Ikem Anibeze, mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga Umar Farouq, ta ce wannan ciyarwar da ake magana tana da banbanci da wacce ake yi a karkashin ma'aikatar walwala da jin kai.

A watan Augusta ne ministan ta ce gwamnatin tarayyar ta kashe N500 miliyan wurin ciyar da yara 'yan makaranta yayin kullen korona.

Ta ce ciyarwar ta 'yan makaranta ce daga aji daya zuwa uku a fadin kasar nan ba ta daliban kwaleji ba.

Ta ce sauran al'amuarn damfarar da suka fito daga ICPC duk basu da alaka da ma'aikatarta, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar

Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC
Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Mannir Jaafaru

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta (ICPC), a ranar Litinin, ta ce ta bankado makuden kudi har N2.67 biliyan na ciyar da 'yan makaranta amma a asusun bankuna masu zaman kansu.

ICPC ta ce kudin da aka waskar zuwa asusun bankuna masu zaman kansu, an bada ne domin ciyar da yara 'yan makaranta amma kuma suna gida.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin taron gangami a kan yaki da rashawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel