Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan

Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan

- Sau da yawa ganin sunan kasa ko kyawawan hotunanta kan sa jama'a su ji sha'awar kai ziyara

- Amma kuma ba kowacce kasa bace take maraba da baki ko son ganinsu baki daya

- Dalilansu kan fara da rashin hatimin shiga kasa ko rashin jirgi kai tsaye har kasar

Kafin ka fara tafiya zuwa wata kasa a fadin duniya, akwai matukar amfani idan ka gane cewa ba dukkan kasashen duniya bane suka maraba da kai ko kuma suke son ganinka.

A saboda haka, dole ne a bincika tare da gano kasashen da ke da wuyar zuwa ko kuma basu maraba da baki.

Dalilansu sukan fara da rashin samun hatimin shiga kasar, rashin jirgi kai tsaye da zai kai ka da sauran dalilai.

1. Libya

Da yawa daga jami'an gwamnati kan bada shawara tare da jan kunne a kan zuwa kasar Libya. Idan kana son shiga kasar, sai dai ta kasar Misra idan ba daga nahiyar Afrika bane.

Babu jirgi kai tsaye da ke kai mutum zuwa Libya daga Ingila ko Amurka, amma kamfanin jragen sama na Afriqyah yana zuwa daga Istanbul zuwa Tripole ko kuma daga Tunis.

2. North Korea

Kasar North Korea bata maraba da baki, kuma za su yi komai da za su iya wurin ganin sun hana jama'a kai ziyara.

Suna bukatar duk bako da ya biya kudin zagayen da zai yi a yayin ziyara. A yayin ziyarar, dole ka ksance tare da mai jagorar.

Rashin ofishin jakadancin kasar a kasashe masu yawa na duniya na nufin cewa sai dai a nemi damar shiga kasar ra China.

3. Turkmenistan

Kafin aminta da shiga kasar Turkmenistan sai ka amince da dan jagora wanda hakan ke da matukar tsada.

KU KARANTA: Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna

Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan
Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan. Hoto daga @Pulseng
Source: Twitter

KU KARANTA: Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

4. Bhutan

A kusan karni 50 da suka gabata, jama'a basu iya ziyartar masarautar Bhutan. A halin yanzu, akwai kamfanonin jiragen sama biyu da ke shige da fice a kasar.

Amma kuma nan dole ne a samu dan jagora wanda dan asalin kasar.

5. Syria

A halin yanzu ana tsaka da rikici a kasar Syria kuma basu bai wa kowa hatimin shiga kasarsu. Kowanne hatimin shiga kasar kan dauka dogon lokaci kafin a bada damar amfani da shi.. Sau da yawa a kan hana hatimin bayan dogon lokaci.

A wani labari na daban, sarkin Brunei, Hassanal Bolkiah, ya kasance daya daga cikin sarakunan duniya masu tarin dukiya.

Kamar yadda Insider ta wallafa, ya taba mallakar dukiyar da ta kai $40 billion (N15,500,000,000,000) a duniya.

Wasu daga cikin yanayin facakar da yake da kudinsa sun hada da tseren motocin kirar Ferrari a cikin dare a babban birnin Brunei, gina gida mai dakuna 1,788 da kuma kashe $20,000 (N7,750,000) domin aski.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel