'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki (Hotuna)

'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki (Hotuna)

- Wasu mayakan Boko Haram da ke yankin arewa maso gabas ta Najeriya sun mika wuya ga dakarun soji

- Hedkwatar tsaro ta sanar da hakan tare da wallafa hotunan 'yan ta'addan da suka mika wuya

- Sun bayyana kansu tare da iyalansu ga bataliya ta 155 da ke Banki

Wasu mayakan ta'addancin Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Banki.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa, ta bayyana hotunan mayakan ta'addancin tare da iyalansu da suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Mayakan ta'addancin tare da iyalansu sun mika kansu ne ga bataliya ta 155 da ke Banki.

'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki
'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki. Hoton daga @DafenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki
'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki. Hoto daga @DefenseInfoNg
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki
'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki. Hoto daga @DefenseInfoNG
Asali: Twitter

A wani labari na daban, babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, tare da matansa hudu, sun mika kansu ga rundunar sojin kasa ta Najeriya, Channels TV ta wallafa.

Hakazalika, an halaka 'yan bindiga bakwai tare da ceto wasu mutum 8 da aka yi garkuwa da su a Fankama da Sabon Layi da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Kastina.

Wannan na kunshe a wani jawabi na shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana yayin jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Duk da Enenche bai bada gamsasshen bayani a kan kwamandan da ya mika kansa ba, ya ce wannan nasarar ta samu ne bayan kokari da jajircewar da dakarun suka bayyana.

"A yankin arewa maso gabas, rundunar Operation Lafiya Dole ta aiwatar da jerin samame ta jiragen yaki da kuma kasa, inda ta dinga bankado maboyar 'yan ta'adda a jihohin Borno, Yobe, Taraba da ADamawa.

"Hakazalika, babban kwamandan da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ke ji da shi, tare da matansa hudu sun mika kansu ga dakarun," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel