Da duminsa: Sabbin mutane 136 sun kamu cutar Coronavirus yau

Da duminsa: Sabbin mutane 136 sun kamu cutar Coronavirus yau

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 136 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Asabar 26 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 136 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-41

Ogun-27

Rivers-19

Abia-10

Oyo-6

Plateau-6

Bauchi-5

Ondo-5

Ekiti-4

Kaduna-4

Edo-3

Ebonyi-2

Bayelsa-1

Delta-1

Osun-1

Yobe-1

Jimillan wadanda suka kamu: 58,198

Jimillan wadanda aka sallama: 49,722

Adadin wadanda suka yi wafati: 1,106

A bangare guda, Uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Aisha, ta ce bullar annobar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mutanen duniya.

Aisha ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Masallacin kasa dake birnin tarayya Abuja, yayin muhadaran murnan cikar Najeriya shekaru 60 da samun yanci.

Yayinda take kira da a kara kaimi wajen yaki da cutar, ta yi kira ga yan Najeriya su taimakawa kasar da addu'an zaman lafiya da cigaba yayinda ake murnan shekaru 60 da samun yanzin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel