Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

- Rundunar sojin saman Najeriya ta ragargaza mayakan ta'addancin Boko Haram masu tarin yawa a Borno

- Rundunar ta samu labarin yadda 'yan ta'addan ke dafifi cikin dare a wani sansaninsu da ke Tongule

- Hakazalika, Operation Hail Storm 2 ta aiwatar da wasu hare-hare a Bone da Isari B Musa inda wasu 'yan ta'addan suka sheka lahira

Samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta'addanci da kuma halaka wasu daga cikin 'yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.

Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa 'yan ta'addan na zama a yankin da dare kadai.

Kamar yadda ya dace, jiragen rundunar sojin saman dauke da bindigogin yaki sun kai hari yankin da dare, inda suka halaka da yawa daga cikin 'yan ta'addan.

A Bone, kusa da yankin Yale-Kumshe, jiragen yakin sun kai samamen bayan tabbataccen bayanin sirri da suka samu.

Jiragen dakarun sojin saman sun sakarwa yankin bama-bama tare da zuba musu ruwann wuta, lamarin da yasa sansanin da wasu mayakan suka halaka.

Hakazalika, a Isari B Musa, da yawa daga cikin 'yan t'addan sun mutu sakamakon harin ba-zata da jiragen yaki suka kai dajin.

KU KARANTA: Na yi babban laifi ga Ubangiji idan ban yi wa Wike godiya ba - Obaseki

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan Boko Haram a Borno (Bidiyo)
Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan Boko Haram a Borno (Bidiyo). Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

A wani labari na daban, babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, tare da matansa hudu, sun mika kansu ga rundunar sojin kasa ta Najeriya, Channels TV ta wallafa.

Hakazalika, an halaka 'yan bindiga bakwai tare da ceto wasu mutum 8 da aka yi garkuwa da su a Fankama da Sabon Layi da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Kastina.

Wannan na kunshe a wani jawabi na shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana yayin jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel