Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)

Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)

- Gwamna Zulum ya cigaba da aikin da ya kaisa Baga inda yan Boko Haram suka kaiwa tawagar jami'ansa hari

- Hotuna sun nuna Zulum a Baga zagaye da jama'a da jami'an tsaro

- Ya lashi takobin cigaba da ayyukansa ba tare da tsoron harin yan Boko Haram ba

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi maganarsa ta farko bayan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar ranar Juma'a.

Legit ta ruwaito muku cewa akalla mutane 30 suka rasa rayukansu a harin da yan ta'addan da ake kyautata zato yan kungiyar ISWAP ne suka kaiwa tawagar jami'an gwamnatin jihar Borno yayinda suke hanyar zuwa Baga.

Majiyoyi biyu sun bayyanawa AFP ranar Asabar cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya ninku daga Juma'a zuwa yau saboda an tsinci wasu gawawwaki.

Wadanda aka kashe sun hada da yan sanda goma sha biyu, Sojoji biyar, yan sa kai hudu da masu farin hula tara. Harin ranar Juma'a ne karo na biyu da za'a kaiwa gwamnan cikin watanni biyu.

A cewar majiyoyin da ke da masaniya game da harin, sun bayyana cewa jami'an gwamnatin sun nufi Baga ne cikin shirin da gwamnatin jihar keyi na mayar da masu gudun hijra gidajensu daga Maiduguri.

Shi gwamnan Borno tuni ya tafi cikin jirgi mai saukar angulu.

A ranar Asabar a Baga, Zulum ya bayyana cewa tsoron harin yan Boko Haram ba zai hanashi cigaba da aikin da yake yi na mayar da yan gudun hijra muhallansu.

"Ba zan ji tsoron hare-hare ba yayinda nike yiwa al'ummata aiki ba," Zulum ya bayyana a shafinsa na Facebook.

DUBA NAN: Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari

Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)
Credit: Egr Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

KARANTA NAN: Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)
Credit: Egnr Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)
Tsoron hari bai isa ya hana ni yiwa al'ummata aiki ba - Gwamna Zulum ya yi maganarsa ta farko bayan harin jiya (Hotuna)
Asali: Facebook

Wannan hari na zuwa ne kwana hudu bayan kisar Kanal DC Bako da yan Boko Haram suka kashe.

A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Bayan Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka kashe, Zulum ya sanar da baiwa iyalan sauran Sojoji uku da aka kashe tare da shi milyan biyu-biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel