Sai da na zub da hawaye ranar zabe - Oshiomole ya yi maganarsa na farko bayan zaben Edo

Sai da na zub da hawaye ranar zabe - Oshiomole ya yi maganarsa na farko bayan zaben Edo

- Tsohon gwamnan jihar Edo ya yi maganarsa na farko tun bayan faduwar jam’iyyar sa a zabe

- Oshiomole ya yi namijin kokarin a akwatin ya hana PDP samun ko kuri’a ko guda

- Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben da tazarar kuri’u sama da duba tamanin

Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomole ya bayyana cewa sai da ya zub da hawaye ranar Asabar da akayi zaben gwamnan jihar Edo.

Godwin Obaseki, governor of Edo and candidate of the Peoples Democratic Party (PDP), had defeated Osagie Ize-Iyamu, his APC rival, in the election.

Za ku tuna cewa gwamna Godwin Obaseki kuma dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ne yayi nasara a zaben.

Duk da cewa jam'iyyun siyasa 14 sukayi takara a zaben, sakamakon ya nuna cewa takaran na tsakanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da All Progressives Congress APC.

A cewar hukumar gudanar da zaben kasa INEC, dan takaran jam'iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki, wanda ya samu kuri'u 307,955 ya lallasa abokin hamayyarsa, Osaze Ize-iyamu wanda ya samu kuri'u 223,619.

Oshiomole na daga cikin wadanda suka yiwa jamiyyar APC da dan takararta, Ize-Iyamu yakin neman zabe.

KARANTA Sarkin Zazzau: Ina sauraron masu zaben sarki su gabatar min da sunaye - El-Rufa'i

A hirarsa na farko tun bayan zaben, Oshiomole ya bayyana yadda ya zub da hawaye yayinda ya ga tsofaffin mata sun jajirce sai sun kada kuri'arsu duk da matsalolin da aka rika samu.

Ya ce maimakon su yi fushi kan yadda na'urar tantance masu zabe ke bata lokaci, hakuri sukayi har sai da suka kada kuri'a.

Ya bayyana hakan ne a hirarsa da GEE Africa TV kuma The Cable ta gano.

Sai da na zub da hawaye ranar zabe - Oshiomole ya yi maganarsa na farko bayan zaben Edo
Sai da na zub da hawaye ranar zabe - Oshiomole ya yi maganarsa na farko bayan zaben Edo
Asali: Getty Images

Mun kawo muku cewa kwanaki uku bayan shan kashi a zaben gwamnan jihar Edo, dan takaran jami'yyar All Progressives Congress APC, Osagie Ize-Iyamu ya gana da jiga-jigan jam'iyyar biyu a Abuja.

Ize-Iyamu ya yi zaman sirri da gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar APC, Mai Mala Buni, da kuma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel