Sarkin Zazzau: Ina sauraron masu zaben sarki su gabatar min da sunaye - El-Rufa'i

Sarkin Zazzau: Ina sauraron masu zaben sarki su gabatar min da sunaye - El-Rufa'i

- A ranar Laraba aka yi addua’r uku na rasuwar marigayi sarkin Zazzau, Shehu Idris

- Majiyoyi sun bayyana cewa kimanin mutane hudu ake sa ran za’a daya cikin su

- Daga akwai Turakin Zazzau, Iyan Zazzau, Yariman Zazzau da Magajin garin Zazzau

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa yana sauraron masu zaben sarki a masarautar Zazzau su gabatar masa da shawarwarinsu kan sabon sarkin da za'a nada.

El-Rufa'i ya bayyana cewa lallai ya lura mutane da dama sun zuba ido kan wanda za'a zaba, kuma saboda haka yayi addu'a Allah ya baiwa masu zaben Sarki hikiman zaban Sarki mai irin dabi'un marigayi Alhaji Shehu Idris.

Mai magana da yawun El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Laraba.

Yace: "Tun da an kammala kwanakin makoki, gwamnatin jihar Kaduna na sauraro cikin yan kwanaki masu zuwa shawararin masu zaben sarki a masarautar Zazzau game da sabon sarki."

"Al'umma su saurari sanarwar gwamnati kuma suyi watsi da jita-jita, kiyase-kiyase da labaran karya."

"Dubi ga yadda yada ra'ayoyin mutane ya janyu kan lamarin wanda zai dane kujerar sauratar Zazzau, El-Rufa'i ya yi addu'a Allah ya baiwa masu zaben sarkin hikima."

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yi tafiya kasar Guinea Bissau gobe:

Sarkin Zazzau: Ina sauraron masu zaben sarki su gabatar min da sunaye - El-Rufa'i
Sarkin Zazzau: Ina sauraron masu zaben sarki su gabatar min da sunaye - El-Rufa'i
Asali: Twitter

Duba nan Sai da na zub da hawaye ranar zabe - Oshiomole ya yi maganarsa na farko bayan zaben Edo

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya rasu, ba ya iya bacci sai ya sha ya sha magani saboda tsananin baƙin ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne wajen taron addu'ar sadakar uku na Marigayin da ya gudana yau Laraba, 23 ga Satumba, 2020, BBC ta ruwaito.

Manyan mutane da dama sun halarci taron addu'ar. Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel