Atiku Abubakar ya yi martani a kan rahoton badakala a Amurka

Atiku Abubakar ya yi martani a kan rahoton badakala a Amurka

- Atiku Abubakar ya karyata rahoton da aka wallafa a cikin 'yan kwanakin nan da ke cewa Amurka na bincike kan wasu hada-hadan kasuwanci masu alaka da shi

- A martanin da ya yi ta bakin kakakinsa, Paul Ibe, Atiku ya ce wannan karya ce da aka dade ana yi kuma ba ta da tushe domin shi da iyalansa ba su saba wata doka ba

- Kakakin na Atiku yace akwai yiwuwar wasu ne kawai ke son kawar da hankulan mutane kan rahoton da Amurka ta fitar na hana wasu mutane shiga kasar ta a kan magudin zabe

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce shi da iyalansa ba su aikata wani laifi ba saboda haka ba su cikin wadanda Amurka ke sanya wa ido ko bincika.

Akwai wani rahoto da aka wallafa da ke cewa Cibiyar Hana Laifukan Kudi, FinCEN da ke karkashin Sashin Kula da Baitul Malin Amurka tana saka ido a kan Atiku da wasu cikin iyalansa.

DUBA WANNAN: Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)

Atiku Abubakar ya yi martani a kan rahoton badakala a Amurka
Atiku Abubakar ya yi martani a kan rahoton badakala a Amurka. Hoto daga Flickr
Source: Twitter

Amma cikin martanin da ya yi a ranar Talata, Kakakin Atiku, Paul Ibe ya ce: "Wannan tsohon zargi ne mara tushe da aka dade ana yinsa."

Ya ce an wallafa rahoton ne domin karkatar da hankalin 'yan Najeriya daga sanarwar da sakataren Amurka, Mike Pompeo ya fitar a baya bayan nan kan haramtawa wasu 'yan Najeriya shiga Amurka saboda magudin zabe.

"Idan ba a manta ba an wallafa wannan karerayin gabanin zaben shugaban kasa na Fabrairun 2019. Mai girma Atiku Abubakar ya nemi izinin zuwa Amurka kuma an bashi, ya tafi a ranar 17 ga watan Janairun 2019.

KU KARANTA: Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno

"Ya sauka a wani otel da ke kusa da Hukumar Shari'a ta Amurka.

"A yayin ziyarar, wasu jami'an gwamnatin Amurka sun gana da shi.

"Ganin cewa an fitar da wannan rahoton kasa da awa 24 bayan zaben gwamnan jihar Edo shima abin tambaya ne da ya dace mutane suyi la'akari da shi.

"Ina son tunatar da al'umma cewa Atiku da iyalansa suna kasuwanci mai tsafta ne bisa dokokin Najeriya da na kasashen waje," in ji shi.

A cewar rahoton da Premium Times ta wallafa, sabbin bayanai sun nuna cewa FinCEN tana bincike a kan wasu hada-hadan kudi da ke da alaka da babban dan siyasan.

A wani labarin, kun i cewa an nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel