Da duminsa: Babu gudu babu ja da baya a kan zanga-zangar farashin man fetur - NLC

Da duminsa: Babu gudu babu ja da baya a kan zanga-zangar farashin man fetur - NLC

- Kungiyar Kwadaga ta Kasa, NLC ta sha alwashin yin zanga-zanga a kan karin farashin man fetur da lantarki da gwamnati ta yi a kasar

- Shugaban kungiyar na kasa, Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan mintuna kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwa na Kungiyar da aka yi a Abuja

- Kwamared Wabba ya ce dukkannin shugabannin kungiyoyin na jihohin Najeriya 36 da na Abuja sun amince da fara yin zanga-zangan daga ranar 28 ga watan Satumba

Da duminsa: Babu gudu babu ja da baya a kan zanga-zangar farashin man fetur - NLC
Da duminsa: Babu gudu babu ja da baya a kan zanga-zangar farashin man fetur - NLC. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

Kungiyar Kwadaga ta Kasa, NLC, ta ce ba za ta fasa zanga zangar da ta shirya yi ba daga ranar 28 ga watan Satumban 2020 bayan gwamnatin tarayya ta ki mayar da tsohon farashin man fetur da lantarki a kasar.

DUBA WANNAN: Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya ce kungiyar za ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi mako mai zuwa bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwar Kungiyar da aka yi a yau Talata a Abuja.

Ya ce shugabannin jihohi 36 na kungiyar da na Abuja dukkansu sun amince da yin zanga-zangar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

A wani labarin daban da Legit.ng ta wallafa, Hukumomin tsaro da suka hada da 'yan sandan, 'yan sandan farar hula, DSS, da jami'an hukumar tsaro da NSCDC sun hana wasu 'yan Najeriya yin zanga-zanga a kan karin farashin man fetur, lantarki da haraji a kasar.

An fara zanga-zangar ne a kofar ofishin Kungiyar 'yan Jarida ta Kasa, NUJ, da ke Farm Centre Road a safiyar ranar Talata a Kano yayin da jami'an tsaro masu yawa suke wurin.

Wata kungiyar kare hakkin al'umma mai suna Joint Action Forum ce ta jagorancin zanga-zangar kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Sanarwar ta shugaban kungiyar, Dr Musa Bashir da Sakatarenta, Abba Bashir Ahmed suka fitar ta yi kira da gwamnatin jihar ta mayar da farashin man zuwa N86 duk lita ta kuma mayar da tsohon farashin lantarkin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel