Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida

Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida

- Jihar Kogi ce kadai a Arewa ta umurci dalibai su koma makaranta bayan tsawon lokaci

- Gwamnatin jihar Kano ta ce har yanzu tana sauraron umurnin gwamnati

- Yawancin jihohin kudancin Najeriya sun bude makarantu kuma sun koma karatu

Makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihohin Legas, Ogun, Osun, Ekiti, da Oyo sun bude ranar Litinin kuma bisa ka'idojin da aka gindaya na kariya daga cutar Korona.

Wakilan jaridar PUNCH sun ziyarci makarantu da dama a yankin kuma sun tabbatar da cewa malamai da dalibai na bin umurnin gwamnati na wanke hannu, amfani da tsummar fuska da baiwa juna tazara.

Bayan watanni biyar da kulle makarantun firamare, sakandare da jami'o'i a fadin Najeriya, abubuwa sun dawo daidai yayinda jihohi sun bude makarantu.

Tuni daliban ajujuwan karshe masu jarabawar WAEC da NECO suka koma makaranta.

DUBA NAN: Bude makarantu: Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohin da suke shirin bude makarantu a Najeriya

Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida
Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Ku bude makarantuku - Gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi dama

A Delta Jami'o'i a jihar Delta sun koma bakin aiki ranar 21 ga Satumba, 2020, watanni biyar bayan rufesu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Majiyoyi daga gwamnatin jihar sun bayyana cewa an yarje da komawan dalibai makarantar ne bayan ganawar gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa da masu ruwa da tsaki.

A Legas gwamnan Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin bude dukkan jami'o'i mallakan gwamnatin jihar daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Asabar, 29 ga Agusta.

Hakazalika a ranar 21 ga Satumba, an bude makarantun firamare da sakandare amma yace har yanzu daliban kasa da firamare su cigaba da zama a gida.

A jihar Osun Gwamnatin jihar ta bude makarantun jihar ranar 21 ga Satumba, 2020.

Kwamishanar ilimin jihar, Funke Egbemode, ta sanar da hakan ne ranar Litinin. A cewarta, an yanke shawarar haka ne a zaman majalisar zartaswar jihar.

A jihohin Ogun, Ekiti da Oyo duk sun koma karatu.

Yayinda wasu iyaye ke nuna damuwarsu bisa lafiyar yaransu, wasu iyayen sun ce babu wani a matsala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel