Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo

Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo

- Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya lashe zaben gwamnan jihar Edo na 2020

- Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar da nasarar Obaseki bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben

- Babban abokin hammayarsa, Fasto Ize-Iyamu na jam'iyyar All Progressive Congress, APC, ne ya zo na biyu a zaben

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da Mista Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Edo a karo na biyu bayan ya yi nasarar doke abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.

Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.

DUBA WANNAN: Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo
Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo
Asali: Twitter

INEC ta sanar da cewa Obaseki ya zama zakara ne a zaben gwamnan bayan samun kuri'u mafi rinjaye na 307,955 inda mai biye masa Ize-Iyamu ya samu kuri'u 223,619.

Wanda ya zo na uku a zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP da kuri'u 323, sai na hudu dan takatar jam'iyyar LP da ya samu kuri'u 267.

Hukumar zaben ta ce adadin masu zabe da aka tantance domin kada kuri'a a jihar 557,443, yayin da adadin kuri'u masu sahihanci 537,407.

Jimillar kuri'un da masu zabe suka kada 550,242, sannan kuri'un da suka lalace kuma 12,835.

KU KARANTA: Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

Jam'iyyu 14 ne suka gabatar da 'yan takara a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.

A wani labarin daban, An nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

An fara nada shi mukamin na shekaru biyu sannan aka sabunta nadinsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mallam Isa Gusau, Kakakin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum wanda shine shugaban kungiyar ya ce an sanar da nadin Abba-Aji ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watar 15 ga watan Satumban 2020 mai dauke da sa hannun Zulum.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel