Zaben Edo: Obaseki ya dauki hanyar nasara yayinda INEC ke shirya sauran sakamakon

Zaben Edo: Obaseki ya dauki hanyar nasara yayinda INEC ke shirya sauran sakamakon

- Hukumar INEC ta saki sakamakon zaben kananan hukumomi 13 a jihar Edo

- Gwamna Godwin Obaseki ya lashe kananan hukumomi 11 yayinda Ize-Iyamu ya ci 2 kacal

- Har yanzu ana sauraron sakamakon sauran kananan hukumomin biyar

Sakamakon da hukumar gudanar da zaben kasan watau INEC ya nuna cewa gwamnan jihar Edo mai ci yanzu, Godwin Obaseki, ne kan gaba da tazarar kuri'u kimanin dubu dari tsakaninsa da na biye da shi, Osagie Ize-Iyamu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Legit.ng ta ruwaito muku cewa an gudanar da zaben gwamnan jihar ne ranar Asabar, 19 ga Satumba, kuma hukumar INEC na tattara sakamakon yanzu.

Channels TV ta ruwaito cewa an sanar da sakamakon kananan hukumomi 13 kuma Obaseki ya lashe guda 11 yayinda abokin hamayyarsa ya ci biyu.

Har yanzu ba'a sanar da sakamakon sauran kananan hukumomin ba.

Jihar Edo na da kananan hukumomi 18.

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

Ga jerin wadanda aka sanar:

1. Karamar hukumar Igueben

APC: 5,189

PDP: 7,870

2. Karamar hukumar Esan ta Arewa maso gabas

APC 6559

PDP 13,579

3. karamar hukumar Esan ta tsakiya

PDP: 10,694

APC: 6,719

4. Karamar hukumar Ikpoba Okha

PDP: 41, 030

APC: 18, 218

5. Karamar hukuma Owan ta gabas

APC: 19,295

PDP: 14,7626.

6. Karamar hukumar Estaka West

APC: 26,140

PDP: 17,959

7. karamar hukumar Egor

APC: 10, 202

PDP: 27, 621

8. Karamar hukumar Esan ta yamma

APC - 7,189

PDP - 17,433

9. karamar hukumar Uhunmwonde

PDP: 10,022

APC: 5,972

10. Karamar hukumar Ovia ta Arewa

APC - 9907

PDP - 16, 987

11. Karamar hukumar Esan south East

APC: 9,237

PDP: 10,563

12. Karamar hukumarsa Oredo

APC: 18,365

PDP: 43,498

13. Karamar hukumar Owan West

APC - 11,193

PDP - 11,485

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel