Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200

Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200

- Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya lashe akwatinsa wa APC

- Akwati mai lamba 001 ta samu kada kuri'ar mutane 1201

- Jam'iyyar adawa ta PDP bata samu ko da kuri'a guda a akwatin gidan Oshiomole ba

Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Aliyu Oshiomole, ya yi nasara a rumfarsa na tazara fiye da na ko ina kawo yanzu a jihar.

Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 1,201 a gunduma ta 10, akwati mai lamba 001 na karamar hukumar Estako West a yau Asabar.

Jam'iyyar PDP ba ta samu kuri'a ko kwaya daya a akwatin gidan Oshiomole ba, bisa sakamakon da aka sanar.

Sakamakon gidan Oshiomole ta baiwa APC dama toshe gurbin da PDP ta zarce mata a karamar hukumar duk da cewa mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu dan gari daya ne da shi.

Tun da akwai gunduma 12 a karamar hukumar Estako West, har yanzu ba za'a iya fadin wanda zai yi nasara tun akwai saura kuri'un da ba'a kirga ba.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda aka biya mutane kudi su kada kuri'a a rumfar zaben Oshiomole, kamar yadda akayi a wasu wurare da dama.

Yan jaridar da suka yi kokarin daukan hoton hakan sun fuskanci wulakanci daga hannun matasan dake wajen.

Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200
Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200
Asali: Twitter

A bangare guda, Dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC a zaben gwamnan jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu ya lashe rumfar zabensa dake gunduma ta 5, garin Iguododo a karamar hukumar Orhionwon.

Ize-Iyamu ta lashe akwatin inda ya samu kuri'u 292 kuma Godwin Obaseki ya samu kuri'u 0.

Hakazalika Dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Godwin Obaseki, ya lashe rumfar zabensa dake akwati ta 17, makarantar firamaren Emokpae, karamar hukumar Oredo.

Yayinda Obaseki ya lashe akwatinsa da kuri'u 184, Ize-Iyamu ya samu kuri'u 62.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel